Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 16:33:45    
Kungiyoyiyn kasashen Ghana da Italiya da Australia sun shiga jerin kungiyoyi 16 mafiya nagarta

cri

Ran 22 ga wata bisa agogon wurin, gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa tana ci gaba a kasar Jamus, rukunoni na E da F sun kammala gasanni na zagaye na karshe, kungiyoyiyn kasashen Italiya da Ghana da Australia sun shiga jerin kungiyoyi 16 mafiya nagarta.

A cikin gasanni na rukuni na E, kungiyar kasar Ghana da ta shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a karo na farko ta lashe kungiyar kasar Amurka da ci 2 da 1, ta zama kungiyar Afirka ta farko da ta shiga jerin kungiyoyi 16 mafiya nagarta a wannan gami. Kungiyar kasar Italiya ta lashe kungiyar kasar Czech da ci 2 da 1, ta zama ta farko a cikin rukuni na E. Kungiyoyin kasashen Czech da Amurka sun koma gida.

A cikin rukuni na F, kungiyoyin kasashen Brazil da Australia sun shiga jerin kungiyoyi 16 mafiya nagarta, kungiyoyin kasashen Japan da Croatia sun kammala ziyararsu a wannan gami, kuma sun koma gida.(Tasallah)