Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 14:47:00    
Firaministan kasar Sin ya yi shawarwari tare da shugaban kasar Tanzania

cri

Wen Jiabao da Jakaya Mrisho Kikwete

A ran 22 ga wata, a birnin Dar es Salaam, firaministan kasar Sin Wen Jiabao wanda ke yin ziyara a Tanzania ya yi shawarwari tare da shugaban kasar, Jakaya Mrisho Kikwete, inda bangarorin biyu suka cimma daidaito a kan kara bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

A gun shawarwarin, Mr.Wen ya ce, kasar Sin za ta inganta da kuma bunkasa hadin gwiwar aminci da ke tsakanin Sin da Tanzania daga fannin habaka hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da dai sauransu, kuma za ta ci gaba da ba da taimako bisa karfinta ga Tanzania a fannonin bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma. Kasar Sin tana kuma shirin ba da taimako wajen gina cibiyar ba da misali ta noma da ta yaki da malariya a Tanzania.

A nasa wajen kuma, Mr.Kikwete ya ce, bangaren Tanzania yana marhabin da kamfanonin kasar Sin da su je Tanzania don zuba jari da kuma sa hannu cikin aikin raya manyan ayyuka da na bunkasa wutar lantarki. Ya ce, Tanzania tana kara mu'amalar siyasa tare da kasar Sin, kuma tana tsayawa tsayin daka a kan matsayin jama'ar kasar Sin a kan batutuwan Taiwan da na Tibet.

Bayan shawarwarin kuma, Mr.Wen da Mr.Kikwete sun kuma halarci bikin daddale yarjejeniyar hadin gwiwar tattalin arziki da ciniki da dai sauran yarjejeniyoyi da ke tsakanin gwamnatocin kasashen biyu.

Mr.Wen ya fara yin ziyarar aiki a Tanzania ne bayan da ya kammala ziyararsa a Afirka ta kudu. Kafin ya tashi daga Afirka ta kudu, bi da bi ne Mr.Wen ya gana da mataimakiyar shugaban Afirka ta kudu Phumzile Mlambo-Ngcuka da kuma babban jami'in zartaswa na ofishin sakatare na 'shirin NEPAD, wato sabon shirin abokai kan bunkasa Afirka', Firminio Mucavele, inda bangarorin biyu suka yi musanyar ra'ayoyi a kan kara ingiza hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka ta kudu da kuma hadin gwiwar da ke tsakanin Sin da Afirka.(Lubabatu Lei)