Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-23 10:59:38    
Jirgin ruwa na Al'adu yana dauke da babbar sha'awar Guangxi kuma ya burge mutanen Beijing

cri

Ko da ya ke a duniya an kasance da kabilu da harsuna da al'adu masu bambanci daban daban , amma ana iya gina gadoji da su , ta yadda za a sa mutanen da suke zaune a wurare daban daban da su fahimci juna da musanya ra'ayoyinsu. Yanzu a nan birnin Beijing ana nune-nunen wake-wake da raye-raye masu cike da halin musamman na kabilar Zhuang ta Jihar Guangxi .

Jihar Guangxi mai ikon tafiyar da harkokin kabilar Zhuang tana kudancin kasar Sin . A wannan yankin ya kasance da kabilar Zhuang da kabilar Han da kabilar Yao da kabilar Miao da kabilar Dong da Kabilar Jing da sauran kabilu 6 . Al'adun kabilu daban daban sun sha bamban da juna tamkar yadda wani jirgin ruwa yake , ya je ko'ina sai ya ga bambancin al'adun .

Kwanakin nan a nan Birnin Beijing , hedkwatar Kasar Sin , ana nune-nune al'adun shahararrun biranen al'adu na kasar Sin da na kasashen waje .

Kogin Rawaya wato Kogin Huanghe shi ne asalin tsofafin al'adun kasar Sin . Duk wadannan sun bayyana kyawawan al'adu masu jawo hankulan mutanen duniya .

Wu Xiaonu , Wakiliyar Rediyon kasar Sin ta ruwaito mana labari cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , a nan kasar Sin tana mai da hankali sosai kan masana'antun al'adu . Gwamnatocin matakai daban daban suna mai da muhimmanci a kansu . Jama'a na bangarori daban daban suna shiga cikin wannan aikin masana'antun . Yanzu larduna da jihohi na kashi 2 cikin 3 na duk kasar Sin sun gabatar da cewar za su kafa masana'antun al'adu da ya zama babbar masana'antarsu . A cikin shirinmu na yau za mu kai ku zuwa Lardin Guangxi dake kudancin kasar Sin don binciken hakikannun abubuwa a wajen yalwata masana'antun al'adu .

Wakiliyarmu ta ce , jirgin ruwan yana da ma'ana biyu. Na farko , yana iya zirga-zirga a ruwa kuma yana da karfi . Kuma ya zo daga Guangxi zuwa Beijing , nan gaba zai je duk duniya. Ma'ana ta biyu shi ne jirgin ruwan yana iya daukar sakamakon gyare-gayre da bude kofa na Guangxi . Kuna yana dauke da zumuncin mutanen kabilu daban daban miliyan 49 na Guangxi zuwa birnin Beijing . A shekarar 2005 , wasannin cartoon da Kamfanin Jiangtong ya wallafa sun mamaye a kudu maso arewacin kasar Asiya . An kiyasta cewa , ya zuwa karshen wannan shekara yawan wasannin katoon zai kai kusan 100 . Wannan ba a iya ganin saurinsu ba a cikin shekaru biyu da suka wuce . Ma iya cewa , bayan da aka fitar da labarun soyayya a hanyoyin sadarwar internet , wasannin kwaikwayon cartoon sun zama sabon salo mai jawo hankulan mutane .

Gwamnatin kasar Sin ta gabatar da sabon tsarin kirkire-kirkire, wannan ba kawai a wajen kimiyya da fasaha ba , har ma a wajen masana'antun al'adu . Yalwatuwar masana'antun al'adu na Jihar Guangxi ta sa mutane suka sauya tsohon tunaninsu kuma ta kawo karfin kirkire-kirkire . Alal misali , Kamfanin Jiangtong ya riga ya zama madugu a wajen wallafa sababbin wasannin cartoon a duniya . Amma duk da haka , Mr. Zhu , babban manajan kamfanin ya ce, nan gaba za su mai da hankali kwarai a kan ingancin wasannin cartoon.(Ado )