Aminai masu sauraro, abun da muke so mu gaya muku, shi ne yanzu ana nan ana gudanar da ayyuka iri daban daban cikin taka tsantsan domin share fage ga yin gagarumin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. Kwanaki baya ba da dadewa ba, a nan Beijing, kwamitin sulhuntawa kan taron wasannin motsa jiki na Olympics na 29 na kwamitin wasannin motsa jiki na duniya ya yi cikakken zamansa na 6, inda aka amince da cewa lallai ayyukan share fage ga yin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Baijing sun gamsar da mutane kwarai da gaske.
Ko kun san, cewa aikin gina dakunan wasannin motsa jiki, wani muhimmin aiki ne yayin da ake gudanar da yunkurin share fage ga shirya gagarumin taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. A duk tsawon lokacin taron, wakilan kwamitin sulhuntawa sun yi rangadin filayen gina dakunan wasannin motsa jiki ciki har da filin wasan motsa jiki mai siffar gidan tsuntsu na kasa da kum:a Cibiyar wasan iyo ta kasa, inda suka ganam ma idonsu babban ci gaban da aka samu wajen gina wassu muhimman gine-gine na wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008.
Shugaban kwamitin sulhuntawar Mr. Hein Verbruggen ya furta, cewa:
'Lallai kyakkyawan halin gina dakunan wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 ya faranta ranmu kwarai da gaske. A ganina, kyakkyawan ginin filin wasannin motsa jiki mai siffar tsuntsu na kasar Sin na Beijing ya shahara a duniya kamar yadda dakin wake-wake na Sydney yake'.
Bisa shirin da kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya fito da shi, an ce, tun daga shekarar da muke ciki, an rigaya an juya muhimman ayyukan share fage ga yin taron wasannin motsa jiki na Olympics daga matakin tsara shirye-shirye zuwa na gudanarwa a zahiri. Bayan da aka saurari rahoton kwamitin shirya wasannin Olympics na Beijing, sai Mr.Verbruggen ya fadi cewa, takamaiman shirye-shiryen ayyuka iri daban daban da bangaren Beijing yake gudanar da su, sun cimma burinmu sosai, wanda kuma yake son sauraron shawarwari masu amfani daga kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na duniya.
Sa'annan Mr. Verbruggen ya bayyana, cewa kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics na duniya ya yi farin ciki da ganin yadda kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing yake yin hadin gwiwa sosai tsakaninsa da babbar hukumar shirye-shiryen kiyaye muhalli ta Majalisar Dinkin Duniya da mashahuran kwararru da mashawarta na duniya wadanda suka gwanance a fannin ilmin kiyaye muhalli, da bai wa juna wutar yula, da sayar da tikiti da kuma na shirya bukukuwa da dai sauran manyan harkoki.Mr. Hein Verbruggen ya kara da, cewa :' Wajibi ne mu nuna wani hakikanin abu, cewa mun gamsu kwarai da gaske da ganin irin salon aiki da ake bi ; kuma wajibi ne mu amince da, cewa dukan ma'aikatan kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics da muke cudanya da su, su mutane ne na-gari wadanda kuma suke da halin kirki'.
A karshe dai , Mr. Verbruggen ya jaddada,cewa abun da ya faranta ran dukkan wakilan kwamitin wasannin motsa jiki na Olympics, shi ne bangaren kasar Sin yana mai da hankali sosai kan kyakkyawan tasirin da taron wasannin motsa jiki na Olympics zai kawo wa Beijing har duk kasar Sin.Ya furta, cewa :'Kila a karo na farko ne a cikin zukatanmu muke jin, cewa kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing yana mai da hankali kwarai da gaske kan kayan tarihi da taron wasannin motsa jiki na Olympics zai bari a nan Beijing ; kuma mun ganam ma idonmu yadda suke aiwatar da hasashen da suka kaddamar da shi a kan cewa : ' Taron wasannin motsa jiki na Olympics mai launin kore-shar, da taron wasannin motsa jiki na Olympics na kimiyya da fasaha da kuma taron wasannin motsa jiki na Olympics na zamantakewar al'adu', wato ' Green Olympics, High-tech Olympics, and People's Olympics' a Turance.
Mr. Liu Qi, shugaban kwamitin shirya taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing ya yi jawabi a gun taron, inda ya ce, kwamitin zai kara yin cudanya tare da kungiyoyin da abun ya shafa, da ci gaba da ilimantar da samari matasa da yawansu ya kai miliyan 400 na kasar Sin a fannin wasannin motsa jiki na Olympics da kuma kara kiyaye muhalli.( Sani Wang)
|