Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-22 09:55:17    
Rukunoni na C da D sun kammala dukan gasanni

cri

Ran 21 ga wata bisa agogon wurin, ana cin gaba da yin gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a kasar Jamus. Rukunoni na C da D sun kalmmala gasanni na zagaye na karshe, a karshe dai kungiyoyin kasashen Argentina da Holland da Portugal da Mexico sun shiga cikin jerin kungiyoyi 16 mafi nagarta lami lafiya.

A cikin gasannin da aka yi a cikin rukunoni na C, kungiyar kasar Argentina da kungiyar kasar Holland sun yi kunnen doki, ba su taka wani kallo ba, kungiyar kasar Cote d'ivoire ta lashe kungiyar kasar Serbia and Montenegro da cin 3 da 2, kungiyoyin kasashen Argentina da Holland sun zama na farko da na biyu a cikin rukuni na C; a cikin gasannin da aka yi a cikin rukuni na D, kungiyar kasar Portugal ta lashe kungiyar kasar Mexico da cin 2 da 1, ta ci nasara a cikin dukan gasanni 3 na rukuni na D, ta haka ta zama ta farko, kungiyar kasar Mexico ta zama ta 2; kungiyar kasar Angola da kungiyar kasar Iran sun yi kunnen doki da 1 da 1, ba su shiga jerin kungiyoyi 16 masu nagarta ba.(Tasallah)