Ran 21 ga wata da yamma, a birnin Cape Town, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao da shugaban kasar Afirka ta Kudu Mr. Thabo Mvuyelwa Mbeki sun yi shawarwari.
A gun shawarwarin, Mr. Wen ya bayyana cewa, yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka ya dace da moriyar bangarorin 2. Har kullum kasar Sin tana yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da ciniki, bisa ka'idojin yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da neman samun bunkasuwa tare. Kasar Sin ta riga, ta kuma ci gaba da daukan matakai na ragewa da soke basusuka da rage kudin kwastan da sa kaimi kan zuba jari da dai sauransu don sa kaimi kan bunkasuwar cinikin da de tsakanin kasashen Sin da Afirka mai daidaituwa. Kasar Sin tana son ba da taimakon bunkasuwa ga kasashen Afirka, da taimake su wajen daga matsayinsu na fasaha da tafiyar da harkoki, ta yadda za su kara karfinsu na samun bunkasuwa mai dorewa.
A nasa bangaren kuma, Mr. Mbeki ya ce, kasar Afirka ta Kudu ta mayar da kasar Sin wata abokiya ce ta muhimman tsare-tsare da ke kiyaye zaman lafiya da ingiza bunkasuwa. Ba ta ganin cewa, kasancewar kasar Sin a Afirka barazana ce gare ta ba. Kasashen Afirka ta Kudu da Sin suna da moriya bai daya, kasarsa za ta ci gaba da himmantawa ga habaka yin hadin gwiwa da kasar Sin da kuma karfafa huldar abokantaka ta muhimman tsare-tsare a tsakaninsu.
Bayan shawarwarin, kasashen Sin da Afirka ta Kudu sun rattaba hannu kan 'tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu kan zurfafa huldar abokantaka ta muhimman tsare-tsare' da sauran takardu 12.
Mr. Wen ya bayyana wa kafofin yada labaru cewa, shugaba Mbeki da shi sun sami fahimtar juna sosai kan batun cinikin kayayyakin saka da ke tsakaninsu, bangarorin 2 suna ganin cewa, ko kusa wannan ba ya yi illa ba a kan yin hadin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da ciniki daga dukan fannoni.(Tasallah)
|