Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-22 08:46:44    
Firaminista Wen Jiabao ya yi shawarwari da shugaban kasar Afirka ta Kudu

cri

Ran 21 ga wata da yamma, a birnin Cape Town, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao da shugaban kasar Afirka ta Kudu Mr. Thabo Mvuyelwa Mbeki sun yi shawarwari, sun kuma rattaba hannu kan 'tsarin ka'idoji na yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu kan zurfafa huldar abokantaka ta muhimman tsare-tsare'.

Mr. Wen ya bayyana cewa, yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Afirka ya dace da moriyar bangarorin 2. Har kullum kasar Sin tana yin hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannonin tattalin arziki da ciniki , bisa ka'idojin yin zaman daidai wa daida da moriyar juna da neman samun bunkasuwa tare. Kasar Sin ta riga, ta kuma ci gaba da daukan matakai na ragewa da soke basusuka da rage kudin kwastan da sa kaimi kan zuba jari da dai sauransu don sa kaimi kan bunkasuwar cinikin da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka mai daidaituwa. Kasar Sin tana son ba da taimakon bunkasuwa ga kasashen Afirka, da taimaka musu wajen daga matsayinsu na fasaha da tafiyar da harkoki, ta yadda za su kara karfinsu na samun bunkasuwa mai dorewa.

a nasa bangaren kuma, Mr. Mbeki ya ce, kasar Afirka ta Kudu ta mayar da kasar Sin wata abokiya ce ta muhimman tsare-tsare da ke kiyaye zaman lafiya da ingiza bunkasuwa. Ba ta ganin cewa, kasancewar kasar Sin a Afirka barazana ce gare ta ba. Kasashen Afirka ta Kudu da Sin suna da moriya bai daya, kasarsa za ta ci gaba da himmantawa ga habaka yin hadin gwiwa da kasar Sin da kuma karfafa huldar abokataka ta muhimman tsare-tsare a tsakaninsu.(Tasallah)