Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-21 22:05:45    
Wen Jiabao ya isa birnin Cape Town domin fara yin ziyara a kasar Afirka ta Kudu

cri
A ran 21 ga wata da yamma, agogon wurin, bayan da ya gama ziyararsa ta aiki a kasar Angola, Wen Jiabao firayin ministan kasar Sin ya isa birnin Cape Town, babban birnin kafa dokoki na kasar Afirka ta Kudu domin fara yin ziyarar aiki a kasar.

Wen Jiabao ya kai wa kasar Afirka ta kudu ziyara ne bisa gayyatar da shugaba Thabo Mbeki na kasar Afirka ta Kudu ya yi masa. A cikin jawabin da ya bayar a rubuce bayan da ya isa filin jirgin sama na Cape Town, Mr. Wen ya ce, burin da yake son cimmawa a cikin wannan ziyara shi ne karfafa zumuncin da ke kasancewa a tsakanin Sin da kasar Afirka ta kudu da kara amincewa da juna kan harkokin siyasa da kara yin hadin guiwa irin ta moriyar juna har da yunkurin neman bunkasuwa tare.

Mr. Wen ya ce, bayan kafuwar dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da kasar Afirka ta kudu tun daga shekarar 1998, bangarorin biyu sun samu sakamako da yawa sakamakon yin hadin guiwa a tsakaninsu a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adu da dai sauransu. (Sanusi Chen)