Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-21 20:43:59    
Gwamnatin kasar Sin na kokarin gudun saurin bunkasa tattallin arziki kasar da ake yi ba kamar yadda ya kamata ba

cri

Yanayin gudanar da harkokin tattalin arzikin kasa da ake yi tun daga farkon wannan shekara har zuwa yanzu, lallai ya bayyana alamun da gwamnatin kasar Sin take damuwa a kai. Bisa kididdigar da aka yi, an ce adadin kudaden da aka samu daga sarrafe-sarrafen aikin kawo albarkar cikin gida wato GDP a cikin watanni uku na farkon wannan shekara ya zarce kashi 10 cikin kashi 100 bisa na makamancin lokaci na shekarar bara sakamakon yawan jarin da aka zuba da kuma yawan makudan kudade da aka samu daga kayayyakin shigi da fici ; Ban da wannan kuma, yawan jarin da aka zuba ta hanyar yin amfani da kadarorin duk zamantakewar al'ummar kasar da kuma yawan rancen kudin kasar Sin wato Renminbi da aka samar daga watan Afrilu zuwa watan Mayu na shekarar da muke ciki sun karu karuwar gaske. Wassu masana tattalin arziki sun yi hasashen, cewa rage saurin zuba jari da kuma samar da rancen kudi da ake yi ba kamar yadda ya kamata ba, wani muhimmin abu ne mai muhimmanci dake tabbatar da yalwatuwar tattalin arzikin kasar Sin lami-lafiya.

Wani rahoton kidaya da hukumar gwamnatin kasar Sin ta bayar ya bayyana, cewa yawan jarin da aka zuba ta hanyar yin amfani da kadarorin duk zamantakewar al'ummar kasar ya dara kashi 30 cikin 100 idan an kwatanta shi da na makamancin lokaci na shekarar bara ; Ban da wannan kuma, adadin rancen kudin da aka samar ya karu da kusan Renminbi Yuan biliyan 800 bisa na shekarar bara. Game da wannan lamari, wani shahararren masanin kimiyya daga Kolejin zamantakewar al'umma da kimiyya na kasar Sin Mr. Yuan Gang ya yi kashedin, cewa lallai ya kasance da saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin ba kamar yadda ya kamata ba. Mr. Yuan Gang ya furta ,cewa :' A takaice dai, an ci gaba da samun saurin bunkasa tattalin arzikin kasar Sin da aka yi ba kamar yadda ya kamata ba daga watan Janairu zuwa watan Mayu na wannan shekara ; kuma yawan jarin da aka zuba ya zarce kashi 30 cikin kashi 100 bisa na shekarar bara ; Bugu da kari kuma, yawan kudin da aka samu daga kayayaykin masarufi a watan Mayu na shekarar da muke ciki ya karu da kashi 14.2 cikin kashi 100 idan an kwatanta shi da na makamancin lokaci na shekarar bara. Lallai ba mu taba ganin irin wannan hali ba cikin shekaru fiye da 10 da suka gabata.

Wannan dai abu ne da gwamnatin kasar Sin take damuwa a kai. A gun taron din-din-din da majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta shirya har sau biyu a kwanakin baya ba da dadewa ba, firayim minista Wen Jiabao ya nemi sassan da abun ya shafa da su rage girman matakin samar da yankunan da ake bukata domin gina manyan cikakkun ayyuka da kuma na gine-ginen biranen kasar ; Dadin dadawa, firaminista Wen Jiabao ya jaddada, cewa ya kamata a ba da jagoranci ga bankunan kasar wajen kayyade yawan rancen kudin da sukan samar cikin matsakaici da kuma dogon lokaci, ta yadda za a rage saurin zuba jari ta hanyar yin amfani da kadarorin kasar da kuma samar da rancen kudi.

Jama'a, manufar kudi da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa ta fi jawo hankulan mutane. A ran 28 ga watan Afrilu na wannan shekara, bankin tsakiya na kasar Sin ya kara yawan ruwan bashi ga wadanda suke bukatar rancen kudi. Lallai wannan ya kara kawo wahala ga wadanda suke bukatar rancen kudi.

Mr. Ba Shusong, kwararre a fannin kudi daga cibiyar nazarin harkokin raya kasa ta majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana, cewa:

' Dalilin da ya sa aka dauki wannan mataki, shi ne domin rage yawan kudin Renminbi da ake samarwa sannu a hankali da kuma rage yawan kudin da ake ma'amala da shi a cikin hannun jama'a.'

Wassu masana tattalin arziki sun bayyana, cewa saurin karuwar jarin da aka zuba da kuma rancen kudin da aka samar daga watan Afrilu zuwa watan Mayu na wannan shekara, wannan dai ba ya nufin cewa wai gwamnatin kasar Sin ba ta samu kyakkyawan sakamako ba wajen daidaita harkokin bunkasa tattalin arzikin kasar daga dukkan fannoni. Sa'annan sun jaddada, cewa ya kamata gwamnatin kasar ta ci gaba da yin matukar kokari wajen shawo kan kasuwannin hada-hadar cinikin gidaje da kuma yin kwaskwarimar tsarin ma'aunin musanye-musanyen kudin Renminbi.( Sani Wang )