Da farko, za mu bayyana muku tambayoyi biyu dangane da gasar samun kyaututtuka da muka shirya a wannan gami. Tambaya ta daya ita ce, wasiku nawa ne masu sauraro suka aiko wa Rediyo Kasar Sin a shekarar 2005? Tambaya ta biyu kuwa ita ce, yanzu cikin harsuna nawa ne gidan rediyo kasar Sin ke watsa shirye-shirye ga masu sauraro na kasashen duniya?
A kwanakin baya ba da dadewa ba, wata ma'adanar bakin kwayar ido ta kasar Sri Lanka wadda ta shahara a duniya ta sami wata takardar da malam Indrananda Abeysekara, dan birnin Colombo, hedkwatar kasar ya aika mata, inda ya yi tambayar ko zai iya ba da kyautar bakin kwayar idonsa bayan ya rasu. A cikin takardarsa, Malam Indrananda ya rubuta cewa, idan hali ya yi, zai ba da kyautar bakin kwayar idonsa ga wani Basine. Game da dalilin da ya sa haka, sai ya bayyana cewa,
"ni wani mai sauraro ne da ke sha'awar gidan rediyo kasar Sin ainun. Na fahimci kasar Sin ta hanyar wannan rediyo, kuma na kulla aminci tare da kasar Sin, yanzu, ina kishinta kwarai."
Malam Indrananda shi ne shugaban kungiyar masu sauraron gidan rediyo kasar Sin ta kasar Sri Lanka, yana ta kokari wajen yin ma'amala tsakanin kasashen Sri Landa da Sin har cikin shekaru da yawa da suka wuce. Bisa kokarin da ya yi ne, birnin Changsha, fadar gwamnatin lardin Hunan da ke a tsakiyar kasar Sin da birnin Kaludara na kasar Sri Lanka suka zama birane masu abuta da juna. Ya taba samun lambar girmamawa ta aminci da gwamnatin kasar Sin ta ba shi, haka nan kuma kungiyar sada zumunta ta kasar Sin tare da kasashen waje ita ma ta ba shi "lambar girmamawa ta manzon aminci na kasar Sri Lanka", dadin dada wa shugaba Hu Jintao na kasar Sin da sauran manyan shugabannin kasar sun taba ganawa da shi kuma sun nuna masa yabo. Bisa kokarin da yake yi, yanzu, yawan kulob-kulob din masu sauraron rediyo kasar Sin ya karu har ya wuce 700 a kasar Sri Lanka.
Sashen Swahili na rediyo kasar Sin yana da masu sauraro da yawa a kasashen Afrika kamar Kenya da Tanzaniya da Uganda da Burundi da sauransu. Malam Huang Yanling, ma'aikacin wannan sashe ya bayyana cewa,
"masu sauraronmu suna kokarin aiko mana takardu. Wasunsu su kan aiko mana takarda daya a ko wace rana, inda suka bayyana abubuwa filla-filla a kan shirye-shirye da muka watsa a wannan rana, da labaru da wadanda suka karanta labarun, da kuma shawarwari da ra'ayoyinsu a kan shirye-shiryenmu. A wani sa'i kuma suna aiko mana takardu guda biyu a yini daya. Irin wannan kokari da masu sauraronmu ke yi ya burge mu kwarai, kuma ya kara mana kwarin guiwa sosai wajen gudanar da aikinmu na watsa labaru."
Shirin koyon Sinanci yana daya daga cikin shirye-shiryen musamman da gidan rediyo kasar Sin ke yi. Tarin masu sauraronmu sun ji Sinanci ne ta hanyar sauraron wannan shiri, bayan haka kuma sun koya wa danginsu ko aminansu ko dalibansu Sinanci, ta haka an kara yadada al'adun kasar Sin a kasashe daban daban.
Malama Sakurai Kimiko, mai sauraronmu ta kasar Japan ta taba shafe shekaru biyu tana nazarin Sinanci a kasar Sin. Bayan komawarta a gida, ta kara zurfafa ilminta na Sinanci ta hanyar rediyo kasar Sin, sa'an nan tana koyar da Sinanci a wasu makarantun sakandare da makarantun koyon harsuna, haka zalika 'yan makarantarta ma suna sha'awar shirye-shiryen rediyon kasar Sin. Yanzu, duk lokacin da ita da dalibanta suka sami damar zuwa birnin Beijing, ba makawa za su bakunci rediyo kasar Sin. Malama Sakurai Kimiko ta ce, "a duk lokacin da ni da dalibaina muka sami damar zuwa birnin Beijing, ko shakka babu, za mu bakunci sashen Japananci na gidan rediyo kasar Sin, mu yi hira da ma'aikatan sashen nan cikin Sinanci ko Japananci. Mun ji dadi ainun. Bayan da dalibanta suka koma gida, sun nuna wa 'yan makarantunsu hotuna da suka dauka cewa, ziyartar gidan rediyo kasar Sin abu ne mai ban sha'awa. Idan kun sami sarari, to, wajibi ne, ku kai ziyara a gidan rediyon nan. Ta haka yayin da sauran 'yan makarantar suka sami damar zuwa birnin Beijing, dole ne, su ma su kai ziyara a gidan rediyon kasar Sin. Ta haka mu masu sauraronmu da ke ma'amala da gidan rediyo kasar Sin kullum sai kara karuwa suke yi. "
A bene na biyu na babban ginin gidan rediyon kasar Sin, an gwada kayayyakin kyauta masu dimbin yawa da masu sauraronmu suka aiko mana a cikin manyan kabad. Daga cikinsu akwai kayayyakin sassaka na Afrika da 'yan tsana masu ban sha'awa da kasar Japan ta yi da kwakwa, da kayayyakin kida da kasar Vietnam ta yi da gora, da karamin samfurin husumiya da ake kira "Eiffel Tower" a birnin Paris na kasar Faransa, da kwallon kafa na kasar Italiya wanda shahararrun taurari 'yan wasan kwallon kafa na duniya suka sa hannu a jikinsa da dai sauransu. Daga cikinsu, akwai wani abu da ya fi jawo hankulan mutane shi ne wani kundi mai kauri da wani mai sauraron rediyo kasar Sin ya shirya don shiga gasar samun kyaututtuka da rediyo kasar Sin ya shirya.
Madam Shi Li daya daga cikin shugabannin ofishin kula da harkokin masu sauraro na rediyon kasar Sin ta bayyana cewa, yawan masu sauraro na rediyon kasar Sin ya yi ta karuwa a cikin shekaru 65 da suka wuce. Ta ce, "a sakamakon ci gaba da aka samu a cikin shekaru 65 da suka gabata, masu sauraronmu sun riga sun game ko ina cikin duniya. Kulob-kulob din masu sauraronmu ma sun yi ta karuwa. Yanzu, yawansu ya riga ya kai 3600. Mu kan shirya bukukuwa masu kayatarwa a tsakaninmu da wadannan kulob-kulob a ko wace shekara. Yawan wasiku da muka samu a shekarar 2005 ya karu har ya wuce miliyan 2 da dubu 170. Haka zalika ya zuwa tsakiyar shekaru 1970, gidan rediyo kasar Sin yana watsa wa masu sauraro na duniya shirye-shiryensa cikin harsuna 48."
Jama'a masu sauraro. Yanzu za mu maimaita muku tambayoyi da muka shirya game da gasar samun kyaututtuka da muka shirya a wannan gami. Tambaya ta farko ita ce, wasiku nawa ne masu sauraro suka aiko wa Rediyo Kasar Sin a shekarar 2005? Tambaya ta biyu kuwa ita ce, yanzu cikin harsuna nawa ne gidan rediyo kasar Sin ke watsa shirye-shirye ga masu sauraro na kasashen duniya?
To, jama'a masu karatu. Muna maraba da ku shiga gasar nan. Addireshimu shi ne Hausa Service CRI-24; China Radio International; P.O. Box 4216, Beijing, China, ko Lagos Bureau, China Radio International, P.O.Box 7210, Victoriya Island, Lagos, Nigeria, haka nan kuma adireshinmu na E-mail shi ne Hausa @Cri.com.cn. (Halilu)
|