Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-21 17:28:05    
Ana kiyaye al'adun gargajiya a gundumar Chang Yang ta lardin Hubei

cri

Garin Ziqiu shi ne wani karamin gari da tsaunuka suke kewayensa a gundumar Chang Yang ta kabilar Tujia mai ikon aiwatar da harkokin kanta . Rera wakar "Sayelhe" shagali ne da aka yi na nuna al'adar kabilar Tujia, a kan kira shagalin nan da cewar wai yin tsalle-tsalle domin bikin ta'aziya. A lokacin da dangin wasu mutane ya mutu, mutane ba su yi kuka tare da hawaye ba, amma akashin haka, suna daga sautin muryarsu suna rera wakoki tare da raye-raye, ta hanyar nan ne don bayyana zaman rayuwarsu na kasancewa cikin halin sakin jiki tare da hakuri da kome. Bayan binciken da aka yi , an tabbatar da cewa, an riga an yada al'adar nan a kauyukan kabilar Tujia cikin shekaru fiye da dubu, amma dayake mutanen kabilar Tujia suna zama a wuraren da ke barbazuwa sosai, shi ya sa ba safai a kan ga irin wannan bikin da ake yi na rera wakar "Sayelhe" ba, abin da kuka saurara a baya shi ne wasannin da dakin kula da harkokin al'adu na gundumar nan ta shirya. Wani tsohon dan wasan fasaha mai suna Tian Zhenguo ya bayyana cewa, mu ne 'yan wasannin fasaha da muka zo daga jama'a, wake-wake da raye-rayen da muke yi na gargajiya ne, muna tunawa da su a cikin kwakwalwarmu sosai da sosai, sa'anan kuma mun yada su daga zuri'a zuwa zuri'a, ba mu yi kwaskwrima a kansu ko kadan ba, na gargajiya ne kawai. In ana bikin ta'aziya ko bikin aure, sai mu rera wakar yadda muka ga dama.

Wakar "Sayelhe" tana daya daga cikin abubuwa uku masu daraja sosai na kabilar Tujia, sauran biyu da na uku su ne wakar da aka rera a kan tsaunuka wato da yarenmu ake kiran shi "Shange" da kuma kide-kide na kudu. Wakar waka ce da aka rera tare da dagaggen sauti , kuma ba a yi wakar tare da wani ado ba, sai bisa tsarin halittu kawai, Kide-kide na kudu na da dadin ji sosai .

Tamkar yadda hanyoyin da aka bi na yaduwar al'adun gargajiya da ba na kayayyaki ba , abubuwa guda uku masu daraja sosai na kabilar Tujia su ma sun taba fuskantar bacewa, har zuwa yanzu dai, ricikin nan yana kasancewa,samari sun fita waje don samun aikin yi daya bayan daya, tsofaffin 'yan wasan da wuya ne suke iya samun masu bin sawunsu , kuma ana kan shigar da al'adun waje da na zamani sosai , sa'anan kuma kara kyautatuwar sharudan aikin sarrafe-sarrafe da zaman rayuwa a zamantakewar al'aumma na kauyukan gargajiya ya lalata muhallin yin ma'amala ta tsohuwar hanyar rera wakoki da dai sauransu. Amma abin farin ciki shi ne, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin kasar Sin da jama'a suna ta kara mai da hankali ga kiyaye fasahohin wasannin gargajiya da yaduwarsu. Garin Ziqiu shi ma yana daya daga cikin yankunan musamman guda tara na kiyaye al'adun gargajiya.

Ban da al'adun gargajiya da ba na kayayyaki ba, bisa matsayinta na haifar da kabilar Tujia, gundumar Chang Yang ita ma tana da wadatattun kayayyakin tarihi a kasa. Wani shahararren wurin tarihi da ke tanade da dutse mai suna Xianglu ya bayyana al'adun tagulla na kafin shekaru dubu 3 ko dubu hudu. Wani shugaban dakin nune-nune na gundumar Changyang mai suna Luo Jianping ya bayyana cewa, yawan kayayyakin tarihi da dakin nune-nunenmu ya tanada ya wuce dubu 30, yawancinsu an same su ne a lokacin da aka gina wata tashar ba da karfin lantarki, wadannan sun ba da ajiyayyun kayayyaki mafi muhimmanci ga yin binciken masomin al'adun kabilar Tujia.(Halima)