Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-21 16:56:39    
Shugaban kasar Angola ya yi shawarwari tare da Wen Jiabao

cri
A ran 20 ga wata, a birnin Luanda, babban birnin kasar Angola shugaban kasar Angola Jose Eduardo Dos Santos ya yi shawarwari tare da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao wanda ke yin ziyara a kasar, inda bangarorin biyu suka amince da habaka hadin kai tsakaninsu bisa tushen daidai wa daida da moriyar juna domin neman samun bunkasuwa tare.

A cikin shawarwarin, shugaba Dos Santos ya bayyana cewa, kasar Angola tana maraba da kamfanonin Sin da su zo kasar don zuba jari, kuma tana so ta karfafa yin cudanya da hadin gwiwa tsakaninta da bangaren Sin daga dukkan fannoni. Ban da wannan kama ya ce, kasar Angola tana goyon bayan manufofin da Sin ke bi kan harkokin Afirka, tana son yin kokari domin ingiza dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Daga wajensa, firayim minista Wen Jiabao ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin ta nuna wa kasar Angola yabo sabo da tana goyon bayan kasar Sin daya tak a duniya, kuma tana nuna goyon baya ga kasar Angola wajen ayyukan sake gina kasar bayan yaki. Bugu da kari kuma Wen Jiabao ya ce, bangaren Sin zai ci gaba da kara hadin kai tsakaninsa da bangaren Angola a fannonin muhimman ayyuka da sadarwa da makamashi, haka kuma bangaren Sin yana so ya bayar da taimako ga Angola bisa karfinsa, kuma ya karfafa zuriyar kamfanonin Sin da su je Angola domin zuba jari.(Kande Gao)