Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-21 15:37:18    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki (15/06-21/06)

cri

A ran 18 ga watan nan, hadaddiyar kungiyar Sinawa mazauna kasar Kwatdibuwa ta shelanta, cewa Sinawa mazauna wurin sun ba da kudin karo-karo da yawansu ya kai kudin yammacin Afrika wato Franc 900,000 wato dolar Amurka 1,800 ga taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. Ana gudanar da wannan harkar ba da kudin karo-karo ne har zuwa karshen wannan wata. Kansilan ofishin jakadancin kaar Sin dake kasar Kwatdibuwa Mr. Wu Weirong ya furta, cewa kudin karo-karo da Sinawa 'yan kaka gida suka samar ko yana da yawa ko ba yawa, wannan dai ba abu ne mai himmanci ba, abu mai muhimmanci shi ne shiga wannan harka da suka yi don bayyana hasashen " wasannin motsa jiki na Olympics na zamantakewar al'adu" da gaske.

A makon jiya, an ci gaba da gudanar da gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa na shekarar 2006 tsakanin rukuni-rukuni da ake yi a kasar Jamus. Ya zuwa ran 19 ga watan nan, akwai kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasashen Jamus, da Ecuador, da Ingland, da Argentina, da Holland da kuma Brazil da suka samu damar shiga gasar zagaye na biyu ta tace gwani. Za a kammala dukkan gasanni na mataki na farko ne a ran 24 ga watan nan, agogon Beijing. Kungiyar kasar Sin ba ta samu damar shiga wannan gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da ake yi ba a wannan gami.

A ran 19 ga watan da muke ciki, 'yar wasan kwallon tenis ta kasar Sin mai suna Li Na ta sauya tarihin wasan kwallon tenis na kasar Sin saboda ta zama ' yar wasa ta farko da ta shiga jerin ' yan wasa dake kan matsayin gurabe 30 na farko a duniya, wadanda Hadaddiyar Kungiyar Wasan Kallon Tenis ta Sana'a ta Mata wato WTA ta amince da su. Ban da wannan kuma, kila za a mayar da ' yar wasa wato Li Na a matsayin gogaggiyar 'yar wasa a gun hadaddiyar gasar wasan kwallon tenis da za a yi a birnin Wimbledon na kasar Burtaniya a shekarar da muke ciki. Yin haka, lallai zai sake kago tarihin wasan kwallon tenins na kasar Sin.

An yi gasar gudun famfalaki wato Marathon ta 20 ta kasa da kasa a birnin Da Lian dake arewacin kasar Sin. Dan wasa mai suna Ma Lijun na kasar Sin ya zama zakara a gun gasar tsakanin maza; kuma abokiyarsa mai suna Zhu Xiaolin ta zo ta daya a gasar da aka yi tsakanin mata. ' Yan wasa sama da 10,000 daga kasashe da jihohi fiye da 30 sun halarci gasar.

(Sani Wang )