Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 19:22:56    
Shawarwari tsakanin Wen Jiabao da Sassou-Uguesso da kuma Mvou ba

cri

Firaminista Wen Jiabao na kasar Sin ya yi shawarwari tare da shugaba Denis Sassou-Nguesso da kuma firaminista Isidore Mvouba na Jamhuriyar Kongo daya bayan daya jiya da maraice a Brazaville, inda suka yi musanye-musanyen ra'ayoyi kan yadda za a kara kyautata dangantakar abuta ta muhimman tsare-tsare tsakanin kasashen biyu.

Mr. Wen Jiabao ya furta, cewa bangaren kasar Sin yana mai da hankali sosai kan yadda za a bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu cikin dogon lokaci, kuma yana so ya yi kokari tare da bangaren kasar Kongo Brazaville wajen ingiza yunkurin hadin gwiwa na hakika da ake yi tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban. Ban da wannan kuma, bangaren kasar Sin yana fatan za a kara tuntubawa tsakanin bangarorin biyu a fannin siyasa , da kuma samo wani sabon salon hadin gwiwa da za a bi ta hanyar ba da gudummowa daga gwamnati da kuma yin hadin kai tsakanin kamfanoni da ma'aikatu.

A nasa bangaren, Mr. Nguesso ya bayyana, cewa kulla huldar abuta ta muhimman tsare-tsare tare da kasar Sin, wani zabe ne da ya wajaba ga kasar Kongo Brazaville. Ya kuma fadi, cewa bangaren kasarsa yana so ya kara yin hadin gwiwa tare da kasar Sin a fannin siyasa da na tattalin arziki, da kuma ba da taimakon juna a Majalisar Dinkin Duniya da sauran hukumomin kasa da kasa har a kan muhimman maganganun tsakanin kasa da kasa da na shiyya-shiyya.

Yayin da Mr. Wen Jiabao yake yin shawarwari tare da takwaransa Mvouba, ya furta, cewa ya kasance da boyayyen babban karfin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Kongo Brazaville a fannin tattalin arziki. Bangaren kasar Sin zai sa kaimi ga kamfanoni da ma'aikatu na kasar Sin da su zuba jari a kasar Kongo Brazaville.

Mr. .Mvouba ya furta, cewa bangaren kasar Kongo Brazaville yana mai da hankali sosai kan yalwata dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma zai dauki matakai masu yakini don aiwatar da yarjejeniyoyi daban daban da bangarorin biyu suka rattaba hannu a kai. A karshe dai, Mr. Mvouba ya sake nanata, cewa gwamnnatinsa za ta ci gaba da bin ka'idar kasar Sin daya tak a duniya da kuma yin adawa da kowane irin yunkurin samun 'yancin Taiwan da ake gudanar. ( Sani Wang )