Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 18:00:45    
Jami'an Afrika sun ce, kasar Sin ta ba da taimako ga bunkasuwar Afrika

cri
Mai ba da shawara na fadar firayin ministan ta kasar Togo, wanda ke halartar taron kara wa juna sani da aka shirya a nan birnin Beijing ya yi farin ciki sosai matuka da samun labarin cewa, kungiyar kwallon kafa ta kasarsu ta saka kwallon farko a gasar cin kofin duniya da ake yi a kasar Jamus ta yanzu. Ya ce, "wannan shi ne karo na farko kasar Togo ta shiga gasar cin kofin duniya, kasar Sin ce ta ba da babban taimako kan wannan, sabo da filin wasan da ta gina."

Wannan jami'i ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Sin ta ba da taimako samar da gine-gine da yawa a kasar Togo. Wani filin wasa da kasar Sin ta ba da taimako kan ginawa, ya kasance fili mai kyau ga jama'ar kasar Togo wajen shirya gasar kwallon kafa, da kuma sauran wasanni, haka kuma an ingiza bunkasuwar wasan kwallon kafa na kasar cikin sauri. A shekarar da muke ciki, da farko kungiyar kwallon kafa ta wannan kasar da ke yammacin Afrika, wadda yawan mutanenta ya kai kamar miliyan 5 ta shiga gasar cin kofin duniya.

Wasu jami'an da ke halartar taron kara wa juna sani na muhimman jami'ai na kasashen Afrika 11 da bangaren Sin ya shirya su ma suna da ra'ayi daya. Muhammed Hasan Ahmad, wani jami'in da ya zo daga kasar Djibouti ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka wuce, kasar Sin ta ba da taimako ga kasar wajen gina wata cibiyar wasanni, da kuma wani filin wasa mai dauke da mutane dubu 20. "Yanzu, samari su kan yi wasan kwallon kafa da motsa jiki a lokacin hutu, haka kuma yawan aikata laifuffuka ya ragu." Kasar Djibouti tana gabashin Afrika, bayan da ta samu yancin kai a shekarar 1977, kasar Sin ce kasa ta farko da ke ba da taimako gare ta.

Mr. Ahmad ya soma nazarin tarihin kasar Sin a shekaru 18 da suka wuce, ya ce, " me ya sa ana kasancewa da dangantakar musamman a tsakanin kasar Sin da Afrika? Kuma me ya sa mun fi kaunar kasar Sin? Na taba yin tunani kan wannan a cikin dogon lokaci."

"Sabo da kasar Sin ta ba da taimako ba tare da sharuda ba, kuma ba ta taba bukatar mu koyon Sinnanci ba ko fatali da yancin kai ba."

"Kasar Sin ta nuna girmamawa gare mu wajen yancin kai, da ikon mallaka, da kuma hanyoyin da muke zabi."

"Kasar Sin ta ba da taimako sosai kan bunkasuwar Afrika, kuma bunkasuwar Afrika tana bukatar taimako irin wannan."
Gaba daya jami'ai masu zuwa daga kasashen Burundi, da Cameroon, da Congo Brazzaville, da Djibouti, da Gabon, da Guinea, da Nijer, da Ruwanda, da Chadi, da kuma Togo, da dai sauransu kasashen Afrika suka gayawa maneman labaru kamar haka.

Muhimmin batu na wannan taron kara wa juna sani da za a shafe kwanaki 14 ana yinsa shi ne, "gina al'ummar kasashe masu zaman jituwa". Ban da birnin Beijing kuma, wadannan jami'an Afrika za su kai ziyara ga biranen Kunming da Xiamen, da kuma sauran wurare.

Mr. Ahmad ya ce, bisa matsayinta na wata kasa mai tasowa, kasar Sin ta samu sakamako sosai wajen fannin tattalin arziki, da na bunkasuwar al'umma, wannan kuma yana da ma'ana sosai garemu wajen koyarwa.

Shekarar 2006 shekarar cika shekaru 50 da kasar Sin da Afrika suka kulla huldar jakadanci. A cikin wadannan shekaru 50 da suka wuce, kasar Sin ta ba da taimako ga Afrika kan ayyukan tattalin arziki da bunkasuwar al'umma kusa da 900, wannan ya sa jama'ar Afrika sun samu hakikanin moriya."

Jami'ai masu halartar wannan taron kara wa juna sani dukansu sun bayyana cewa, bunkasuwar dangantakar da ke tsakanin Afrika da kasar Sin tana ingantuwa sosai. Suna fatan za su iya jawo jari mafi yawa daga kasar Sin.