Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 17:37:01    
A sha shayi a birnin Chengdu na kasar Sin

cri

Birnin Chengdu fadar gwamnatn lardin Sichuan ne da ke a kudu maso yammacin kasar Sin. 'Yan birnin Chengdu suna sha'awar shan shayi a dakunan shan ruwan shayi.

A cikin dakunan shan shayi na birnin Chengdu, ana tadin duniya, ana yin tattaunawa kan harkokin kasuwanci, samari da 'yan mata kuma suka soyayya a tsakaninsu. Idan wani ya sami damar sa kafa cikin birnin nan, to, zai ga dakunan shan shayi a ko ina cikin duk birnin.

Wani dakin shan shayi da ke daf da gadar kudu a kan kogin Dujiang na birnin nan ya shahara sosai a duk birnin Chengdu. Malam Wu Qing, mai dakin shan shayin nan ta bayyana cewa, "ana iya samun duk ire-iren shahararrun shayi na wurare daban daban na kasar Sin a dakinmu. A kan ji dadin shan shayi a dakinmu mai fadi sosai. Don haka dakinmu yana samun karbuwa daga wajen masu shan shayi."

A birnin Chengdu, ana kiran masu aikin hidima na dakin shan shayi da sunan "likitocin shayi". Dalilin da ya sa haka shi ne domin bayan da wadannan masu aikin hidima suka dade suna yin aikinsu, su kan cudu da jama'a masu yin sana'o'i daban daban, sai ilminsu ma ya karu sosai fannoni daban daban. Haka nan kuma su kan kware wajen zuba ruwan shayi daga buta mai dogon baki na mita 1 cikin kofuna domin masu shan shayi.

Ban da wannan dakin shan shayi na Malama Wu Qing, kuma akwai wani dakin shan shayi daban da ake kira Wenxuange cikin Sinanci shi ma ya shahara a birnin Chengdu. Wannan daki yana da bene biyu. An mayar da bene na farko da ya zama dakin shan shayi irin na gargajiyar kasar Sin, bane na biyu kuma an mayar da shi da ya zama irin na Turai. Ban da 'yan birnin Chengdu, masu yawon shakatawa na kasashen waje da yawa su ma suna sha'awar zuwa dakin nan don shan shayi. Malama Clandia Perle wadda ta fito daga kasar Switzerland ta bayyana cewa, "wannan ne karo na farko da na sha shayi a wannan dakin shan shayi. Kafin wannan, na taba shan shayi a dakunan shan shayi da dama, amma na fi sha'awar kayayyakin gargajiya da aka yi amfani da su wajen kayatar da dakin nan, sa'an nan kuma halin da ake ciki a dakin ma yana da kyau kwarai."

Yanzu, dakunan shan shayi na birnin Chengdu sun riga sun sami manyan sauye-sauye musamman ma kayayyakin shan shayi. Alal misali, 'yan kasuwa da yawa suna sha'awar zuwa dakunan shan shayi don yin tattaunawa a kan harkokin kasuwanci, su kan so su sha shayi mai tsada, a cikin irin wannan hali ne, sai aka fara yin amfani da kofuna irin na duwatsu masu daraja. Idan an sa ganyayen shayi masu launin tsanwa a cikin irin wadannan kofuna, an zuba tafasasshen ruwa a ciki, to, nan da nan ganyayen shayi sai su kumbura su tashi kan ruwan. Amma jim kadan, sai ganyayen shayin nan su kwanta a karkashin kofunan nan. Ruwan nan suna da dadin sha kuma da kamshi.

Manoma da ke zama a karkarar birnin Chengdu suna sha'awar shan wani irin shayin daji da ke tsira da kansa. Irin wannan shayi yana da daci. Da Malama Han Lin, 'yar birnin Chengdu ta tabo magana a kan irin wannan shayi, sai ta bayyana cewa, "manoma da ke zama a karkarar birninmu sun saba da shan irin wannan shayi. Wannan shayi ya kasance tamkar magani domin inganta lafiyar jiki. Kuma manya da yara maza da mata kan iya shan irin wannan shayi don inganta lafiyar jikunansu."

Dakin shan shayi ya kasance tamkar wurin hira ne ga 'yan birnin Chengdu, a nan ne kowa da kowa ke iya gwada kwarewarsa a fannin iya magana. Idan masu yawon shakatawa sun sami damar zuwa birnin Chengdu, to, ya kamata, su shiga cikin dakin shan shayi don ganam ma idanunsu abubuwa masu ban sha'awa da ake yi a dakin nan. (Halilu)