Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-20 11:08:15    
(Sabunta)Wen Jiabao, firayin minstan kasar Sin ya kai ziyara a Jamhuriyar kasar Congo

cri

Wakilin Kamfanin dillancin labarum Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 19 ga watan nan da yamma , Wen Jiabao, firayin minstan kasar Sin ya isa birnin Brazzaville , hedkwatar kasar Congo kuma ya fara yin ziyarar aiki a Jamhuriyar kasar Congo .

A cikin rubutaccen jawabin da Mr. Wen ya yi a Filin jiragen sama , ya ce , yana fatan ziyararsa ta wannan karo za ta kara fahimtar juna da habaka hadin kan tattalin arziki da ciniki , ta yadda za a bunkasa dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Congo zuwa sabon mataki .

A wannan rana Mr. Wen ya yi shawarwari da Denis Sassou Nguesso , shugabvan kasar Congo (Brazzaville). Bayan da aka kawo karshen shawarwarin , Mr. Wen ya bayyana wa manema labaru cewa , lokacin da kasar Sin take ba da taimako ga kasashen Afrika , tana hada taimakon tattalin arziki da taimakon fasaha . Babban nufinta shi ne don inganta karfin yalwatuwa na Afrika ita kanta .

Mr. Wen ya jaddada cewa , a cikin hadin gwiwa tsakanin kudu da kudu da na tsakanin kasar Sin da Afrika , kasar Sin ba ta moriyar son kai ba . Ko yaushe tana tsaya kan zaman daidai wa daida da moriyar juna , kuma ba ta tsoma baki cikin harkokin gidan kowace kasa . Ban da wannan kuma ya sanar da cewa , gwamnatin kasar Sin ta tsai da kudurin ba da taimakon tsabar kudi dalar Amurka miliyan daya ga aikace-aikacen kiyaye zaman lafiya na Kungiyar kasashen Afrika a wurin Darfur na kasar Sudan , sa'an nan kuma za ta kai agajin nuna jin kai na kudin Sin RMB Yuan miliyan 20 ga shiyyar Darfur don sassauta yawan wahalolin da jama'ar wannan shiyyar suke sha .(Ado)