Wakilin Kamfanin dillancin labarum Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 19 ga watan nan da yamma , Wen Jiabao, firayin minstan kasar Sin ya isa birnin Brazzaville , hedkwatar kasar Congo kuma ya fara yin ziyara a Jamhuriyar kasar Congo .
A cikin rubutaccen jawabin da Mr. Wen ya yi a Filin jiragen sama , ya ce , a cikin 'yan shekarun da suka shige , shugabannin kasashen biyu suna mai da hankula sosai han huldar zumunci dake tsakaninsu . Yanzu huldar tana ba da sabon karfi kuma sun sami sakamakon hadin gwiwa a fannoni daban daban . Mr. Wen ya bayyana cewa , yana fatan ziyararsa ta wannan karo za ta kara fahimtar juna da habaka hadin kan tattalin arziki da ciniki , ta yadda za a bunkasa dangantaka tsakanin kasar Sin da kasar Congo zuwa sabon mataki . (Ado)
|