Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-19 19:48:58    
Cin abinci ta hanyar kimiyya ya iya yin rigakafin ciwon sankara na hanji

cri

A shekaru misalin 20 da suka wuce, yawan kamuwa da ciwon sankara na hanji yana karuwa a yawancin kasashen duniya. Wasu sakamakon bincike masu dumi dumi sun nuna cewa, kamuwa da wannan ciwo yana da nasaba da kyautata zaman rayuwa da tsare-tsare da al'adar cin abinci da dai sauransu. A takaice dai, mai yiwuwa ne cin abinci ya haifar da ciwon sankara na hanji. To, wane iri abinci ne za su haddasa kamuwa da ciwon sankara na hanji? Yaya mutane suka kyautata tsare-tsaren cin abinci don yin rigakafin ciwon nan? Yau ma, za mu dan tabo magana kan wannan batu.

Mr. Ye Xianquan mai shekaru 62 da haihuwa yana fama da ciwon sankara na hanji na ajali. Game da dalilin da ya sa mai yiwuwa ne zai haddasa kamuwa da ciwon sankara na hanji, yana ganin cewa, babban dalili shi ne cin abinci ba yadda ya kamata ba, ya ce,'ba safai na kan ci kayayyakin lambu da kuma abubuwan da ke cike da zare, wato fiber a Turance ba. Na yi aiki a Hong Kong tun daga shekarar 1982 har zuwa shekarar 1986. A lokacin nan na fara cin abinci masu sauri, kamarsu abincin da ake bayar a cikin dakunan cin abinci na McDonald's da KFC, sa'an nan kuma, na fara son cin man shanu da cuku.'

Al'adar cin abinci da Mr. Ye ya taba bi a Hong Kong ta yi daidai da ta mutane da yawa a yanzu, suna son cin abincin da aka gyare su sosai da sosai, amma sakamakon bincike ya nuna cewa, irin wadannan abinci suna da nasaba da kamuwa da ciwon sankara na hanji.

Saboda bayan da aka gyare su sosai da sosai, abinci su kan yi cike da kiba, amma ba su da zare da yawa. Binciken kimiyya ya shaida cewa, cin abinci masu kiba da yawa, amma marasa isasshen zare ya zama babban sanadi ne wajen kamuwa da ciwon sankara na hanji. Darekta likita madam Yang Yufei, wadda ke aiki a ckin sashen ciwace-ciwacen sankara na asibiti na Xiyuan na Beijing, ta bayyana cewa,'kiba tana kushe da wasu abubuwan da ke haddasa kamuwa da ciwon sankara, ban da wannan kuma, bayan da kiba mai yawa ya shiga cikin jikin mutum, matsarmama ta kara samar da gishiri na musamman, wanda bayan da ya wuce hanji, ya haifar da wasu abubuwan da ke haddasa kamuwa da ciwon sankara.'

Abinci masu kiba da yawa da mutane suka ci kullum shi ne nama iri daban daban. an sami sakamakon bincike cewa, idan wani ya ci nama na shanu ko na alade gram dari 5 a ko wace rana, to, yawan yiwuwar kamuwa da ciwon sankara na hanji gare shi ya fi na wadanda ba safai su kan ci nama ba da kashi 30 zuwa kashi 40 cikin dari. Shi ya sa kwarerru sun shawarci cewa, ya fi kyau a ci naman sa ko na alade da yawansu bai kai gram dari 3 ba. Sa'an nan kuma, sun ba da shawarar cin naman tsuntsaye da kifaye a maimakon cin naman sa da na alade kullum.

Wani babban dalili daban da ya sa abincin da aka gyara su sosai da sosai su haifar da ciwon sankara na hanji shi ne zaren da ke cikin irin wadannan abinci sun bata da yawa, a lokacin da ake gyara su, amma zare abu ne mai amfani wajen hana kwayoyin ciwon sankara su yi girma.

Masana suna ganin cewa, ya kamata ko wane mutum ya ci zaren da ke cikin abinci gram 20 zuwa 30 a ko wace rana. A kan ci shinkafar da ba a goge ta ba, da masara da gero da alkama da dai sauransu, a maimakon cin shinkafa da gari kullum, wadanda aka gyara su sosai da sosai. Abincin da ke cike da zare su ne 'ya 'yan itatuwa da kayayyakin lambu, kamar su karas da wake da abincin dankali da dai makamantansu. Ya fi kyau a ci su duka, kada a fi cin wasu daga cikinsu, ta yadda za a kiyaye daidaituwa na jikin mutum.

Ban da wannan kuma, abincin da aka soya suna da saukin haifar da ciwon sankara na hanji. Wu Yu, wani likita na sashen ciwace-ciwacen sankara na asibiti na Xiyuan, ya yi bayanin cewa,'mutane masu yawa suna sha'awar cin abincin da aka soya, amma a zahiri kuma, wannan bai kamata ba. Lokacin da wani yake dafa abinci, mai ya yi hayaki, wato yawan zafinsa ya wuce digiri 160, mai ya rabu, ya fito da wasu abubuwan da ke haifar da ciwon sankara.'

Ban da abincin da aka soya kawai ba, bai kamata a ci abincin da aka gasa ko kuma aka ajiye cikin gishiri, ko kuma wadanda ke cikin gwangwanaye kullum ba. Kada a ci dukan abincin da muka ambata a baya da yawa kuma cikin dogon lokaci.(Tasallah)