
Ran 18 ga wata bisa agogon wurin, an kammala gasanni uku na wasan kwallon kafa na cin kofin duniya da ake yi a kasar Jamus.
A cikin gasar da aka yi a tsakanin kungiyar kasar Korea ta kudu da ta kasar Faransa wadda ita ce zakara a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da aka yi a shekarar 1998, kungiyoyin biyu sun yi kunnen doki da 1 da 1.
A cikin farkon rabin gasar, Thierry 'dan wasa na kungiyar kasar Faransa ya ci gwal, amma a karshen rabin gasar, Park Ji Sung 'dan wasa na kungiyar kasar Korea ta kudu ya ma ya ci gwal. Yanzu, kungiyar kasar Korea ta kudu ta ci maki 4, tana zama nambawan a kungiyar G.
A cikin gasanni biyu da aka yi a kungiyar F, kungiyar kasar Brazil ta lallasa ta kasar Austrilia da ci 2 da ba nema. Kungiyar kasar Japan da ta kasar Croatia sun yi kunnen doki.
|