Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-19 10:38:27    
Firaministan kasar Sin ya isa Ghana bayan da ya kammala ziyara a Masar

cri

A ran 18 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya kammala ziyararsa a kasar Masar, kuma ya isa birnin Accra don yin ziyarar aiki a kasar Ghana.

A cikin jawabin da Mr.Wen ya bayar a rubuce bayan da ya isa filin jirgin sama, ya ce, akwai nisa sosai a tsakanin kasashen Sin da Ghana, amma jama'ar kasashen biyu suna da zumuncin gargajiya mai zurfi a tsakaninsu. Ya ci gaba da cewa, gwamnatin kasar Sin tana darajanta aikin bunkasa huldar aminci da hadin gwiwa a tsakaninta da kasar Ghana, kuma tana son samun ci gaba kafada da kafada tare da bangaren Ghana, don bude wani sabon shafi dangane da hadin gwiwar aminci a tsakanin kasashen biyu.

A ran nan, yayin da yake ziyara a kasar Masar, bi da bi ne shugaban kasar Hosni Mubarak da kuma shugaban majalisar jama'ar kasar Ahmed Fathy Sorour suka gana da Mr.Wen. Mr.Mubarak ya bayyana cewa, 'tsarin ka'idar inganta muhimmiyar huldar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Masar' da bangarorin biyu suka kulla a ran 17 ga wata tana da muhimmanci a wajen bunkasa huldar da ke tsakaninsu a nan gaba. Ya kuma yi farin ciki sabo da ci gaba da habaka fannonin hadin gwiwa da ake yi tsakanin kasashen biyu. Bayan haka kuma, Mr.Sorour ya ce, majalisar dokokin Masar tana son kara yin mu'amala tare da majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, kuma tana son yin kokarin sa kaimi ga hadin gwiwar aminci da ke tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangaren kuma, Mr.Wen ya jaddada cewa, inganta huldar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Masar buri ne da kasar Sin ke neman cimmawa a wajen manufarta a kan Masar. Majalisar jama'ar kasar Sin tana son karfafa mu'amala tare da majalisar jama'ar Masar, kuma tana marhabin da kara samun 'yan majalisar Masar da su zo kasar Sin ziyara, don ba da sabon taimako ga bunkasa huldar da ke tsakanin kasashen biyu.

Kafin ya kammala ziyararsa a Masar, Mr.Wen ya kuma kira taron manema labaru a birnin Alkahira, inda ya yi cikakken bayani a kan manufofin gwamnatin kasar Sin dangane da bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Masar, da Sin da kasashen Larabawa da kuma Sin da kasashen Afirka, ya kuma bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin a kan manyan al'amuran duniya da na shiyya shiyya na yanzu. (Lubabatu Lei)