Daga ran 17 zuwa 18 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya kai ziyarar aiki a kasar Masar. A lokacin ziyarar, kafofin yada labarai na Masar sun nuna kulawa sosai a kan ziyarar Mr.Wen, kuma sun ba da rahotanni da yawa dangane da ziyarar.
Jaridar Al-Gomhouria ta Masar ta ba da rahoto a ran 18 ga wata cewa, a lokacin ziyarar Wen, bangarorin biyu na Masar da Sin sun rattaba hannu a kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da takardar fahimtar juna da dama, kuma sun bude cikakken hadin gwiwa a tsakaninsu a fannin tattalin arziki da ciniki.
Bayan haka kuma, jaridar al-aharm ta kasar ta ba da sharhin da ke da lakabin 'makomar huldar abokantaka da ke tsakanin Masar da Sin', inda ta jaddada cewa, ziyarar Mr.Wen a Masar tana da muhimmanci sosai wajen inganta huldar da ke tsakanin kasashen biyu.(Lubabatu Lei)
|