A ran 17 ga wata da dare a birnin Alkahira, firayin minstan kasar Sin Wen Jiabao, wanda yake ziyarar aiki a kasar Massar, ya ba da kyauta ga 'yan kasar Massar 5 abokai masu arziki na kasar Sin kyautar 'mutumin da ke bayar da muhimmiyar gudummuwa ga dangantakar da ke tsakanin Sin da Massar cikin shekaru 50 da suka gabata'.
Wadanda suka sami irin wannan kyauta sun hada da tsohon babban sakataren majalisar dinkin duniya Boutros Boutros-Ghali da tsohon babban sakataren kawancen kasashen Larabawa Ahmed Esmat Abdel Meguid, tsohon mataimakin firayin ministan kasar Massar kuma shugaban kungiyar sada zumunci da ke tsakanin Massar da Sin Yussef Amin Wali da tsohon ministan ilmi na kasar Massar Houssein Kamel Baha'a El-Din da kuma shahararren likita Kamal Gaugary, wanda ya gabatar da dabarar yin allura ba tare da shafa ruwa ta gargajiya ta kasar Sin zuwa kasar Massar a karo na farko.
A haifi Boutros Boutros-Ghali a shekarar 1922, wanda ya gama karatunsa a jami'ar Alkahira. Mr Ghali ya taba zama ministan diplomasiyya na kasar Massar da kuma mataimakin firayin minista kuma ministan diplomasiyya na kasar Massar. A shekarar 1991, Mr Ghali ya zama babban sakatare na 6 a tarihi na MDD, a halin yanzu dai shi ne shugaban kwamitin kare hakkin 'yan Adam na kasar Massar. Mr Ghali ya taba ziyarar kasar Sin sau da yawa, yana aikin sada zumunci da ke tsakanin Sin da Massar cikin dogon lokaci, a lokacin da yake aiki a matsayin minitan diplomasiyya na kasar Massa, ya sa kaimi wajen kafa kwamitin Sin da Massar, haka kuma a matsayinsa na babban sakataren MDD, Mr Ghali ya bayar da babbar gudummuwa ga kasashe masu tasowa ciki har da kasar Sin. An taba mayar masa da ya zama 'dan birnin Dalian na kasar Sin mai daraja.
An haifi Ahmed Esmat Abdel Meguid a shekarar 1923, Mr Meguid ya taba karatu a cibiyar nazarin dokoki ta jami'ar Alexandria da jami'ar Paris. Mr Meguid ya taba zama zaunannen wakilin kasar Massar a majalisar dinkin duniya da mataimakin firayin ministan kasar Massar da ministan harkokin waje na kasar. Tun shekarar 1991 zuwa ta 2001, ya zama babban sakataren kawancen kasashen Larabawa. Mr Meguid ya kan sada zumunci da ke tsakanin Massar da Sin, ya taba bayar da babban taimako ga dangantakar abokantaka da ke tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin. A shekarar 1993, Mr Meguid ya taba ziyarar kasar Sin a matsayin babban sakataren kawancen kasashen Larabawa, bisa kokarin da ya yi, kawancen kasashen Larabawa ya kafa ofishinsa a birnin Beijing a watan Agusta na shekarar 1993, wannan kuma yana da ma'ana sosai ga cudanyar da ke tsakanin kasashen Larabawa da kasar Sin.
An haifi Yussef Amin Wali a shekarar 1930, a shekarar 1951, Mr Wali ya gama karatunsa a jami'ar Alkahira. A halin yanzu dai, Mr Wali ya zama shugaban kungiyar sada zumunci da ke tsakanin Massar da Sin. Ya yi shekaru 36 ne yana aiki a matsayinsa na yau, sabo da haka ya taba ganin tarihin bunkasuwar dangantakar abokantaka da ke tsakanin bangarorin biyu.
An haifi Houssein Kamel Baha'a El-Din a shekarar 1932, wanda ya taba karatu a jami'ar likitanci ta Massar. A cikin dogon lokaci, Mr Houssein Kamel Baha'a El-Din ya dukufa wajen inganta cudanya tsakanin Massar da Sin ta fannin ilmi.
An haifi Kamal Gaugary a shekarar 1921, wanda ya taba karatu a cibiyar likitanci ta jami'ar Alkahira. Mr Gaugary ya zama mutum na farko da ya gabatar da dabarar yin allura ba tare da shafa ruwa zuwa kasar Massar.(Danladi)
|