Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 22:46:08    
Wen Jiabao ya yi sharhi kan cinikin man fetur da ake yi a tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri
A ran 18 ga wata lokacin da yake ba da amsa ga wata tambayar da wakiliyarmu ta kai masa a gun wani taron manema labaru da aka yi a birnin Alkahira na kasar Masar, firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya nuna cewa, kasar Sin da kasashen Afirka suna cinikin man fetur a bayyane kwarai bisa ka'idojin moriyar juna kamar yadda aka saba yi.

A cikin 'yan shekarun da suka wuce, wasu kafofin watsa labaru na kasashen waje sun ce, kasar Sin ta raya dangantakar da ke tsakaninta da kasashen Afirka domin samun man fetur da sauran albarkatu daga kasashen Afirka kuma da aiwatar da sabon mulkin mallaka a kasashen Afirka kawai. Game da irin wannan magana, Wen Jiabao ya nuna cewa, "Kowa ya sani, yanzu kasar Sin da wasu kasashen Afirka suna cinikin man fetur. Muna yin irin wannan cinikayya ne a bayyane kuma a fili bisa ka'idojin moriyar juna kamar yadda aka saba yi. Amma yawan kudin cinikayyar man fetur da muka yi da kasashen Afirka bai kai sulusi ba bisa yawan kudin cinikayyar man fetur da wasu manyan kasashe suke yi da kasashen Afirka."

Game da maganar aiwatar da sabon tsarin mulkin mallaka a Afirka, Wen Jiabao ya jaddada cewa, "Tabbas ne ba a iya fadi cewa kasar Sin tana aiwatar da sabon tsarin mulkin mallaka a Afirka ba. Tun daga shekarar 1840, wato shekarar da aka fara yin yaki da miyagun magani na opium, an yi mulkin mallaka a kasar Sin har tsawon shekaru kimanin 110. Al'ummomin kasar Sin sun san zafin da tsarin mulkin mallaka ya kai musu, sun kuma sani cewa dole ne a yi gwagwarmaya da mulkin mallaka. Wannan dalili ne da ya sa muka goyi bayan kasashen Afirka wajen neman 'yancin kai da bunkasuwa."

Daga karshe dai, Wen Jiabao ya ce, "Lokacin da take shan wahaloli iri iri, kasar Sin ta samar wa jama'ar kasashen Afirka taimako wajen shimfida hanyar dogo da ke hade da Tanzania da Zambia. Yanzu kasar Sin tana samun ci gaban tattalin arziki, ba za mu manta da tsofaffin abonkanmu ba. A kasar Sin akwai wani karin magana, wato sarari mai auna gudun doki, haka yau da gobe mai bayyana zuciyar mutum. Tarihi zai tabbatar da kome da kome." (Sanusi Chen)