Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 21:46:38    
Firaminista Wen Jiabao ya kammala ziyararsa a kasar Masar

cri

Ran 18 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya kammala ziyararsa a kasar Masar. A gun taron ganawa da manema labaru da aka yi a birnin Alkahira a ran nan, Mr. Wen ya darajanta huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Masar, ya kuma bayyana matsayin da kasar Sin ke tsayawa a kai kan aikin yunkurin shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya da kuma batun nukiliya na kasar Iran.

Mr. Wen ya bayyana cewa, a cikin shekaru 50 da suka wuce, kasashen Sin da Masar suna taimakawa da goyon bayan juna, sun kulla abokantaka ta 'yan uwa a tsakaninsu, zumuncin da ke tsakaninsu zai ci gaba da zaune da karfi kamar yadda pyramid ke yi.

Game da batun Palasdinu da kasar Isra'ila, Mr. Wen ya ce, gwamnatin kasar Sin za ta taka rawa mai yakini kuma mai amfani kan wannan batu. Game da batun nukiliya na kasar Iran, Mr. Wen ya jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa tsayin daka kan daidaita wannan batu ta hanyar diplomasiyya.(Tasallah)