Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 20:46:34    
Firaminista Wen Jiabao ya sauka Alkahira, ya fara ziyararsa a Masar

cri
Ran 17 ga wata da yamma bisa agogon wurin, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya sauka Alkahira, inda ya fara ziyarar aiki ta sada zumunta a kasar Masar, bisa gayyatar da takwaransa na kasar Masar Mr. Ahmed Nazif ya yi masa.

Da farko, Mr. Wen ya yi shawarwari da Mr. Nazif. Mr. Wen ya bayyana cewa, kasashen Sin da Masar sun kulla huldar dilplomasiyya a tsakaninsu a shekaru 50 da suka wuce, sun bude kofar dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Larabawa, ta hanyar dandalin yin hadin gwiwa na kasashen Sin da Larabawa ne, bangaren kasar Sin yana son gama kanta da kasashen Larabawa da ke kunshe da kasar Masar wajen kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu da kulla huldar abokantaka ta sabon salo ta yin daidai wa daida da moriyar juna da fuskanatar abubuwan da za su wakana a nan gaba a tsakaninsu. Mr. Nazif ya ce, bangaren kasar Masar yana fata zai hada kansa da kasar Sin wajen ingiza bunkasuwar huldar da ke tsakanin kasashen Sin da Larabawa.

Bayan shawarwarin, Mr. Wen da Mr. Nazif sun rattaba hannu kan 'tsarin ka'ida na zurfafa huldar yin hadin gwiwa ta muhimman tsare-tsare a tsakanin kasashen Sin da Masar'.(Tasallah)