Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-18 19:39:07    
Kasar Sin da kasashen Afrika manyan aminai ne abokai ne kuma 'yan-uwa  ne

cri
 

Firaminista Wen Jiabao ya soma yin ziyara a kasashe 7 na Afrika tun daga ran 17 zuwa ran 24 ga watan da muke ciki.

Jarida "Renmin Ribao" ta kasar Sin ta buga wani bayani, wanda ya nuna cewa, bunkasa kyakkyawar dangantakar aminci ta abuta da hadin gwiwa cikin sahihanci, da samun moriya da juna da kuma samun ci gaba tare, wata manufa ce da gwamnatin kasar Sin take aiwarwa ba tare da tsangwama ba game da harkokin waje. Lallai kasar Sin da kasashen Afrika sun rigaya sun zama kyawawan aminai, kuma manyan abokai dake hadin gwiwa cikin sahihanci kuma 'yan-uwa ne masu raba fara daya.

Ban da wannan kuma, bayanin ya ce, cikin shekaru fiye da 50 da suka shige, har kullum gwamnatin kasar Sin takan mai da hankali sosai kan yalwata da inganta da kuma kara karfafa dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afrika. Bayan da aka shiga cikin sabon karni, dangantakar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a fannin siyasa tana nan tana bayyanuwa a kwana a tashi; bugu da kari kuma, hadin gwiwa da ake yi tsakaninsu a fannin tattalin arziki da cinikayya ya shiga wani sabon mataki. Kazalika, dandalin tattaunawa kan hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika, wanda aka kafa shi a shekarar 2000 ya rigaya ya zama tamkar wani tsari mai amfani na yin shawarwari tsakaninsu gaba daya da kuma wani muhimmin dakali na yin hadin gwiwa na hakika.

A cikin shekaru 6 da suka shige, yawan kudin cinikayya da kasar Sin da kuma kasashen Afrika suka samu ya karu zuwa dolar Amurka kimanin biliyan 40 daga biliyan 10 da miliyan 500; kuma yawan gairar kudi da kasar Sin ta samu ya kai dola biliyan biyu da miliyan 400; Dadin dadawa, daya bayan daya, gwamnatin kasar Sin ta cire yawan bassuka na kudin Renminbi Yuan biliyan 10 da miliyan 500 wadanda kasashe 31 da suka fi samun talauci a Nahiyar Afrika suka ci daga wajenta. ( Sani Wang )