Bisa gayyatar da takwaransa na kasar Masar Ahmed Nazif ya yi masa, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya isa birnin Alkahira a ran 17 ga wata da yamma, agogon wurin, kuma ya fara yin ziyarar aiki ta sada zumunta a Masar.
A cikin jawabin da ya bayar a rubuce a filin jirgin sama na Alkahira, Mr.Wen ya ce, a halin yanzu dai, ana fuskantar sabon zarafi a wajen bunkasa huldar da ke tsakanin Sin da Masar, yin kokarin inganta huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare ya dace da babbar moriyar kasashen biyu da ta jama'arsu, haka kuma zai amfana wa zaman lafiya da bunkasuwar shiyya shiyya da na duk duniya baki daya.
An ce, a lokacin ziyarar, Mr.Wen zai gana da shugaban Masar Hosni Mubarak da firaministan kasar Ahmed Nazif da dai sauran kososhin kasar, inda za su yi musanyar ra'ayoyi a kan bunkasuwar huldar da ke tsakanin bangarorin biyu a nan gaba da batutuwan da suke daukar hankulansu duka.(Lubabatu Lei)
|