Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-17 18:22:34    
Firaministan kasar Sin ya kama hanyar yin ziyara a kasashen Afirka 7

cri
A yau 17 ga wata, firaministan kasar Sin, Wen Jiabao ya tashi zuwa kasar Masar, don yin ziyarar aiki a kasar. Daga nan kuma, Mr.Wen ya fara ziyararsa ta mako daya a kasashen Afirka 7.

Lokacin da yake yin ziyara a kasar Masar, Mr.Wen zai gana da shugaban kasar, Hosni Mubarak, kuma zai yi shawarwari tare da takwaransa na kasar, Ahmed Nazif. Shugabannin kasashen biyu za su waiwayi bunkasuwar kasashensu tun bayan da suka kulla huldar diplomasiyya a tsakaninsu a shekaru 50 da suka wuce, kuma za su tattauna yadda za su kara inganta muhimmiyar huldar hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu. Bayan haka, za su kuma daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da al'adu da ba da ilmi da dai sauransu.

Bayan da ya kammala ziyara a Masar kuma, Mr.Wen zai ci gaba da ziyararsa zuwa kasashen Ghana da Congo Brazzaville da Angola da Afirka ta kudu da Tanzania da kuma Uganda.(Lubabatu Lei)