Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-16 21:34:26    
Ina dalilin da ya sa kungiyar tsaro ta Nato ta yi rawar daji bisa babban mataki a Afrika

cri
Daga ran 15 ga wannan wata, rundunar 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato ta soma yin rawar daji cikin hadin guiwa da ke da lakabi haka: Damisar da ke da tsayayyar niyya ta nahiyar Amurka ?6 bisa babban mataki a kasar tsibiran da ke yammacin Afrika wato kasar Cape Verde. Wannan ne karo na farko da kungiyar ta yi rawar daji a Afrika.

Sojoji 7100 da jiragen ruwan yaki 19 na rundunar sojan ruwa da jiragen sama fiye da goma na rundunar sojan sama na rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato sun halarci rawar dajin nan. Daga cikinsu da akwai wata bataliyar kasashe da yawa ta hana tatsitsin da makaman nukiliya masu guba suka yi tare da rundunar sojoji ta kasar Cape Verde. Za a kawo karshen rawar dajin nan a ran 28 ga watan da muke ciki. A cikin makonni  biyu, bisa jagorancin wata babbar hedkwatar ba da umurni ga rawar dajin nan cikin hadin guiwa a teku , rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato ne ke yin aikace-aikacen soja a jere a kasar Cape Verde. Bisa shirin rawar dajin da aka yi, an ce, dawainiyar rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ita ce, mai da  martani da sauri ga al'amuran da suka faru a cikin kasar Cape Verde da shiyyoyin da ke dab da ita, ciki har da bayyana karfin rundunar soja da yadda ake yin aikace-aikacen ceto ba da agaji bayan aukuwar bala'in halitta, da kuma yin yaki ta hanyar ketare tsibirai da kwashe mazaunan da ke zama a tsibiran a lokacin da duwatsu suka yi amon wuta.

Cibiyar watsa labaru ta rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato ta shelanta cewa, makasudin yin rawar daji shi ne don dudduba matsayin jan damara da karfin yaki na rundunar sojoji 'yan ko ta kwana , wato sabuwar hukumar kungiyar tsaro ta Nato da ke nesa da shiyyar Turai. Babban kwamandan sojojin kawancen kasashen Turai na kungiyar tsaro ta Nato James Jones ya bayyana cewa, muhimmin aiki wajen rawar dajin nan shi ne don dudduba karfin rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato wajen yin doguwar tafiya cikin dogon lokaci.

Game da inda za a yi rawar dajin, da farko, kasar Amurka da kasar Faransa ba su sami ra'ayi daya ba, a karshe dai kasashen biyu sun sami ra'ayi daya a kan batun nan, wato sun zabi inda ake yin rawar daji a kasar Cape Verde da ke nesa da babbar nahiyar Afrika.

Game da ainihin makasudin zaben wurin yin rawar daji bisa babban mataki a nahiyar Afrika , ra'ayoyin kasashen duniya suna da bambancin ra'ayi. 'yan kalo na sha'anin soja na kasa da kasa suna ganin cewa, makasudin dudduba karfin rundunar sojoji 'yan ko ta kwana ta kungiyar tsaro ta Nato ba makasudin farko ba ne gare ta, muhimmin makasudinta shi ne don dudduba yadda za a yi yaki da 'yan ta'adda a nahiyar Afrika, kuma za ta shigar da kawancen soja nata cikin nahiyar Afrika.

Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Itar Tass ya bayar, an ce, wata majiyar labarai na ma'aikatar tsaron kasa ta kasar Rasha ta bayyana cewa, kungiyar tsaro ta Nato ta yi rawar daji a haddin ruwa na tekun Pasific wanda jiragen ruwa masu daukar man fetur suke kai da kawowa, muhimmin makasudinta shi ne don sarrafa hanyoyin sama da teku da ke shiyyar haka gurbataccen man fetur da kuma sa ido kan karfin hanyoyin yin sufurin gurbataccen man fetur zuwa kasuwannin duniya . Kasar Cape Verde tana kusa da gabar teku ta yammacin Afrika , kuma wurin nan babban wuri ne da ke fitar da man fetur. Saboda haka kungiyar tsaro ta Nato ta yi rawar daji a nan, ta yi la'akari da manyan tsare-tsare dangane da makamashi a bayyane.

Manazarta sun bayyana cewa, ta hakan za a iya ganin cewa, man fetur da yin adawa da ta'addanci babban makasudi ne da kungiyar tsaro ta Nato ta yi amfani da shi don yin rawar daji bisa babban mataki a Afrika. Wannan ya bayyana cewa, man fetur da yin adawa da ta'addanci manyan jigogi biyu ne da ke sanya kasashen Yamma yin aikace-aikacen soja a halin yanzu.(Halima)