Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-16 18:54:23    
Me ka sani game da baji koli na sana'ar saka ta kasar Sin da aka shirya a lokacin bazara?

cri

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, sanar'ar saka ta kasar Sin ta samu bunkasuwa cikin sauri sosai. Masu sayen kayayyakin saka na kasashen waje da na kasar Sin suna kaunar kayayyakin saka na kasar Sin kwarai. Amma mai yiyuwa ne ba ka sani ba kasancewa akwai jerin baje koli na nune-nunen kayayyakin saka da ake yi a nan birnin Beijing a kowane lokacin bazara na kowace shekara. Idan kana cinikin kayayyakin saka, kuma kana da sha'awar baje kolin kayayyakin saka na kasar Sin, a cikin shirinmu na yau za mu bayyana muku baje kolin kayayyakin saka da aka yi a nan birnin Beijing a watan Maris na shekarar da muke ciki.

A ran 26 ga watan Maris na shekarar da muke ciki, an fara bikin "Makon nune-nunen sabon salon tufafi" na shekara ta 2006 na kasar Sin a nan birnin Beijing. Ana kiran wannan biki cewa "biki ne da ke nuna makomar sabon salon tufafi ga kasuwar tufafi ta kasar Sin. A gun bikin, wani kamfani da ke da tamburan "Chinese Larch" ya bayyana sabbin salon tufafin maza har fiye da guda dari 1. lokacin da take bayyana halin musamman na tufafin da ta zana, Madam Zhao ta ce, "Na hada halayen musamman iri iri a kan wata tufa. Alal misali, na hada kaya maras kauri da kayan fata tare, ko na hada auduga da zare, ko na hada siliki da auduga tare. A ganina, idan kayayyakin da suke da halaye daban-daban sun hadu tare, za a ga sakamako daban-daban. Sannan kuma, lokacin da nake zane-zane tufafin da za a sa lokacin da ake shan iska, na sa wasu halin musamman na tufafin da ake sa lokacin da ake aiki a ofis."

A gun bikin "Makon nune-nunen sabon salon tufafi na Beijing", za a iya sanin makomar sabon salon tufafi ta kasuwar kasar Sin. A waje daya kuma, a gun bikin baje kolin na tufafi da kayayyakin adon tufafi na duniya da aka yi a birnin Beijing, an ga tamburan tufafi fiye da dubu 1 da aka shigo da su daga kasashe da yankuna 18. Wani dan kasuwa wanda ke sayen tufafi da kayayyakin adon tufafi a sari ya yi mamaki ya ce, bayan isowarka, sai ka ga ana da isassun tamburan tufafi iri iri a nan kasar Sin, farashinsu ma ya yi daidai.

Ban da tufafin da ake nune-nune a gun bikin ba, an yi nune-nunen kayayyakin yin tufafi. A gun bikin nune-nunen kayayyakin yin tufafi, masana'antar yin kayayyakin yin tufafi na birnin Xitao na lardin Hubei da ke tsakiyar kasar Sin ta yi nune-nune kayayyakin yin tufafi iri iri daban-daban da yawansu ya kai daruruwa. Zhang Shiliang, direktan wannan masana'anta ya bayyana cewa, "Muna kago wasu sabbin kayayyaki a kowace shekara bisa bukatun da ake nema a kasuwa. Alal misali, a arewacin kasar Sin, yanayi a busashe yake a kullum. Sabo da haka, mu kan samar da kayayyakinmu da ke iya hana wutar lantarki. Yanzu an fi mai da hankali kan kiyaye muhalli. Sabili da haka, mun yi nazari kan fasahar rigakafin cututtuka. A sakamakon haka, yanzu kayayyakin da muka yi sun samu suna sosai a kasuwannin kasashen duniya. Yawan kayayyakin da muka fitar da su zuwa kasashen waje, musamman a kasuwar kasar Japan da kasuwanni kasashen Turai ya kai kashi 40 cikin kashi dari bisa na dukkan kayayyakin da muka yi a kowace shekara."

Jama'a masu sauraro, a nan kasar Sin mutane wadanda suke tafiyar da sana'ar saka su kan fadi cewa, "Birnin Beijing ya fi kyaun gani a watan Maris" domin a wannan wata an shirya bukukuwan nune-nunen kayayyakin saka iri iri a nan birnin Beijing. Sabbin salon tufafi masu kyaun gani suna jawo hankulan mutane sosai. Mr. Sun Huaibing, kakakin kungiyar sana'ar saka ta kasar Sin ya ce, a gun bikin nune-nunen kayayyakin yin tufafi na lokacin bazara, ba ma kawai masana'antu sun iya sayen kayayyakin da suke bukata da kuma sanin sabbin salon tufafi da ke jawo hankunan mutane ba, har ma an iya kara yin hadin guiwa da musanye-musanye a tsakaninsu da na takwarorinsu na ketare. Mr. Sun ya ce, "Ba jerin bukukuwa kawai ba, har ma suna bayyana hadewar dukkan masana'antu na sana'ar saka. Muhimmin abin da muke tunawa shi ne muna fatan masana'antun da ke yin tufafi da masana'antun da ke yin kayayyakin yin tufari za su hada da juna, kuma za a iya kara saurin raya sana'ar saka."

A gun jerin baje koli na nune-nunen kayayyakin saka da aka yi a nan birnin Beijing a lokacin bazara, baki 'yan kasuwa masu dimbin yawa sun halarci bukukuwa kuma sun sayi kayayyakin yin tufafi a sari da suke bukata. Mr. Salge Martin wanda ya zo daga kamfanin Novalin na kasar Faransa da ya fi suna a sana'ar saka ya ce, kamfanin Novalin ya halarci wannan biki a kowace shekara domin yunkurin yin musanye-musanye da hadin guiwa da takwarorin kasar Sin.(Sanusi Chen)