Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-16 18:44:59    
Kofin duniya

cri
Yanzu kuma za mu shere ku da wani bayani mai ban sha'awa game da wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008. Yanzu ana nan ana gudanar da gagarumar gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa a shekarar 2006 a kasar Jamus. Akan yi iirin wannan gasa ne sau daya a ko wadanne shekaru hudu, wadda kuma ta kasance wata gasa ce dake bisa matsayin koli a duniya. Ko da yake kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ba ta samu iznin shiga gasar da ake yi a wannan gami ba, amma masu aikin wasan kwallon kafa na kasar Sin ba su karaya ba, wato ke nan yanzu suna nan suna kokarin koyon fasahohi masu daraja daga wassu kasashe masu karfi a fannin wasan kwallon kafa ta wannan kyakkyawar damar da suka samu a wannan gami don kallon gasannin da ake gudanarwa cikin zazzafan hali.

Jama'a, ko kun san cewa, kungiyar kasar Sin ta taba samu shiga matakin gasar karshe ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2002 da aka yi a kasashen Korea ta Kudu da kuma Japan, amma a karshe dai, ta sha kaye yayin da ta kara da kasar Kuwait a gun gasar zagaye na farko ta shiyyar Asiya. Ko da yake kungiyar kasar Sin ba ta samu shiga wannan gasa da ake yi ba, amma hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta tura kungiyoyi guda shida na duddubawa dake kunshe da mutane kimanin 150, wadanda kuma za su tafi kasar Jamus daya bayan daya don kallon gasannin.

Mr. Ma Chengquan, mamban kungiyar duddubawa ta farko kuma mataimakin daraktan sashen kula da harkokin gasar league-league ta hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ya yi farin ciki matuka da samun damar kallon gasannin da aka yi tsakanin kasar Jamus da kasar Costa Rica, da tsakanin kasar Argentina da Kwatdibwa da kuma tsakanin kasar Mexico da kasar Iran. Abun da ya ji cikin ziciyarsa shi ne lallai ya kasance da babban alhakin dake bisa wuyan 'yan wasan kwallon kafa na kasar Sin. Ya furta, cewa :

' Bayan da muka kalli wasu gasannin da aka yi, sai muka gano, cewa ba ma kawai kasashe masu karfi a fannin wasan kwallon kafa daga Turai da kuma Amurka ta Kudu sun kara daga matsayinsu na buga kwallon ba, har ma ba a tafi an bar kasashen Nahiyar Afrika baya ba. Taron wasannin motsa jiki na Olympics na Beijing a shekarar 2008 ya zama kyakkyawar dama ce gare mu ta kara nuna hikima da kwazo wajen buga kwallon kafa.'

Yayin da kungiyoyin duddubawa na kasar Sin suke kallon gasannin, sun fada wa wakilanmu, cewa dalilin da ya sa kasashen Jamus da Argentina suke kama matsayin gaba a duniya cikin dogon lokaci wajen buga kwallon kafa, shi ne domin suna da nasu halin musamman na buga kwallon ; ko da kasashen Japan da Korea ta Kudu na Asiya ma sun nuna gwanintarsu sosai tare da nuna nasu halin musamman wajen buga kwallo a gun gasar cin kofin duniya da ake yi yanzu. Mr.Ma Chengquan ya fadi, cewa :

'Lokacin da nake kallon gasar cin kofin duniya a wannan gami, na gano cewa dabaru da kuma halin musamman da kungiyoyin balagaggu na wassu kasashen Turai da na Amurka suka nuna wajen buga kwallo sun yi kama da na kungiyoyinsu na matasa. Amma kungiyoyinmu na samari da na kananan yara da kuma na balagaggu ba su taka rawa iri daya ba wajen buga kwallo. Saboda haka, ya kamata hukumar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta tsara wani cikakken shirin muhimman tsare-tsare game da yadda za a kyautata dabaru da kuma fasahar buga kwallo.'

Yayin da kungiyoyin duddubawa na kasar Sin suke kallon gasar wasan kwallon kafa a ake yi a kasar Jamus, sun kuma yi musanye-musanye tare da mutanen da'i'rori daban daban na wasa kwallon kafa daga wassu kasashe. Tsohon mai koyar da 'yan wasan Swiss wato Mr.Christian Gross ya yi mamaki sosai da samun labarin cewa kasar Sin ta tura manyan kungiyoyin duddubawa don kallon gasar cin kofin duniya a wannan gami.(Sani)