Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-15 11:10:27    
Shugabannin kasashe mambobi na kungiyar hadin guiwar Shanghai sun gana da wakilai na kwamitin 'yan kasuwa

cri
Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na" Mu leka kasar Sin"; A ran l4 ga watan nan da muke ciki, a birnin Shanghai, shugabanni na kasashe shida kamar su kasar Sin da Kazakhstan da Kirghstan da Rasha da Tajikistan da Uzbekstan dake halartar taro na shida na shugabannin kasashe mambobi na kungiyar hadin guiwar Shanghai sun gana da wakilai na kwamitin 'yan kasuwa na kungiyar hadin guiwar Shanghai wanda aka kafa ba da dadewa.Gaba daya ne dukkan shugabanni suna gani cewa, kafuwar wannan kwamitin 'yan kasuwa wani babban al'amri ne cikin bunkasuwar kungiyar hadin guiwar Shanghai. Kuma ba shakka zai iya kara karfin bunkasuwar tattalin arzikin kasashe mambobi na wannan kungiya, da daga matsayin zaman rayuwar jama'ar kasashen shiyyar nan. Yanzu, za mu gabatar muku abubuwan filla filla da wakilin rediyonmu ya rubuto mana daga birnin Shanghai;

Jiya da dare da karfe 6 da minti 30, Mr.Hu Jintao shugaban kasar Sin da Mr. A.Nazarbayev shugaban kasar Kazakhstan da Mr.Bakiyev shugaban kasar Kirghstan da Mr.V Putin shugaban kasar Rasha da E.S.Rakhmonov shugaban kasar Tajikistan da shugaban kasar Usbekstan Mr.I.A Karimov sun gana da wakilai na kwamitin 'yan kasuwa na kasashe shida.

Bayan da shugaba Hu Jintao ya saurari bayanin da wakilin kwamitin ya bayar sai ya yi jawabi, ya ce, kafuwar kwamitin 'yan kasuwa ta kago wani dakalin yin cudanya tsakanin 'yan kasuwa na kasashe mambobi shida da yin hadin guiwa da kyau. Yanzu, tattalin arziki na kasashe mambobi shida ya sami bunkasuwa da kyau, kuma za a kara kyautata muhallin zuba jari kan yin ciniki a tsakanin kasashe shida. Da kuma bude manyan kasuwanni tsakanin kasashe mambobi. Duk wannan zai kawo kyakkyawar damar neman bunkasuwa sosai ga kasashe shida.

Bayan da shugaban kasar Sin ya yi jawabi, bi da bi ne shugabanni na sauran kasashe mambobi 5 su ma sun yi magana.

Inda sun nuna kyakkyawar murna ga kafuwar kwamitin 'yan kasuwa na kasashe shida. Shugaban kasar Kazakhstan Mr.Nazarbayev ya ce, babban makasudinmu shi ne nuna tabbaci ga ci gaban zaman al'umma da bunkasuwar tattalin arziki da daga matsayin zaman rayuwar jama'a na shiyyarmu. Kuma ya ce, ya kamata masana'antun da abin ya shafa da bankoki na kasashe mambobi shida su sa muhimmanci ga hadin guiwar da za a yi kan manyan ayyuka, Kuma gwamnatocinmu za mu ba da musu taimako.

Mr.Putin shugaban kasar Rasha ya bayyana ra'ayinsa cewa, hadin guiwar tattalin arziki ita ce babban tushen dake cikin dangantakar tsakanin kasashen duniya. Kuma ya ce, ta hanyar hadin guiwar tattalin arziki, kasashe daban daban za su iya kara yin cudanya bisa tushen  girmama juna da kai wa juna taimako da neman zaman lumana.

Mr.Putin Ya kuma ce, na yi imani cewa, hadin guiwar tattalin arziki ita ce wani muhimmin abu na kara hadin kan tsakanin kasashe mambobi shida na kungiyar nan, Kuma mun riga mun sami wadansu manyan ayyukan yin aikatayya masu kyau. Yanzu mun fara babban sha'aninmu, ya kamata kasashe manbobi daban daban mu yi amfani da wannan kyakkyawar dama. Kuma tare da himma ne 'yan kasuwana kasashe mambobi daban daban za su kara yin aikatayya kan makamashi da sassan zuba jari da na sauran fannoni daban daban.(Dije)