Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-14 17:36:28    
Gasar Kacici-kacici kan "Ni da CRI" (2)

cri

Jama'a masu sauraro, barkanmu da sake saduwa a cikin jerin shirye-shiryenmu na gasar kacici-kacici ta "Ni da Gidan Rediyon kasar Sin". A cikin wannan shiri na yau, za mu bayyana muku tarihin gidan rediyo kasar Sin. Da farko dai, bari mu bayyana muku tambayoyi 4 game da shirin na yau. Na farko shi ne, yanzu gidan rediyon kasar Sin yana da ofisoshin wakilansa guda nawa a duk fadin duniya? Tambaya ta biyu ita ce, harsuna nawa yake amfani da su domin watsa shirye-shirye? Tambaya ta uku ita ne, a wace kasa ce gidan rediyon kasar Sin ya kafa wani rediyon FM na farko? Tambaya ta hudu ita ce, Yaya sunan shafin Internet na gidan rediyon kasar Sin?

Tun karshen shekaru 70 na karnin da ya gabata, kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare kan tattalin arziki da bude kofa ga kasashen waje. Tun wancan lokaci, aikin watsa labaru ga kasashen waje da kasar Sin ta yi ya fara bin hanyar neman bunkasuwa tare da bude wa kasashen waje kofa. Sabo da haka, gidan rediyon kasar Sin ya kara samun maraba daga masu sauraronsa. Lokacin da ake yin sharhi kan sauye-sauyen shirye-shiryen sashen Jamusanci na gidan rediyon kasar Sin, mujallar "Saurara" ta kasar Jamus ta ce, "Wannan iska mai karfi ce da ta zo daga kasar Sin wadda ke da nisa sosai da mu." A sa'i daya kuma, an yaba wa gidan rediyon kasar Sin cewa, "Gidan rediyo ne da aka fi kauna".

Tun shekarar 1980, gidan rediyon kasar Sin ya fara kafa tasoshin wakilansa a kasashen waje a kai a kai. Da farko dai an kafa wani ofishin wakilansa a birnin Tokyo na kasar Japan da ofis daban a birnin Belgrade na tsohuwar Tarayyar Jamhuriyar Yugoslavia. A cikin wakilansa da aka tura su zuwa wadannan ofisoshi a ketare, madam Liu Suyun wadda ta taba yin aiki a kasar Isra'ila har na tsawon kusan shekaru 5 tana daya daga cikin wakilan da suka fi samun girmamawa daga masu sauraro. Madam Liu wadda yanzu ta dawo nan hedkwatar gidan rediyon kasar Sin ta ce, "A watan Oktoba na shekara ta 2000, jim kadan bayan ta da rikici a tsakanin Palesdinu da Isra'ila. Wata rana, mun je zirin Gaza tare da wata tutar kasar Sin kawai. A gabanmu ne, muka ga an harbe wani dan Palesdinu a kan kafarsa, ya fadi, jini ya fito daga kafarsa. Nisan da ke tsakaninmu ya kai wasu mita kawai. Sabo da haka, na gane, mutuwa da rayuwa suna kusa sosai, mai yiyuwa ne irin wannan matsala za ta auku a kanmu."

Ya zuwa yanzu, gidan rediyon kasar Sin ya riga ya kafa tasoshin wakilansa 27 a kasashen waje. Wakilanmu sun iya aiko dukkan muhimman al'amuran da suka faru a duk fadin duniya zuwa hedkwatar gidan rediyon cikin lokaci. Sannan kuma, yanzu gidan rediyon kasar Sin yana watsa shirye-shirye iri iri har na tsawon sa'o'i fiye da 780 a harsuna 48 a kowace rana. Sakamakon haka, harsunan da gidan rediyon kasar Sin ke amfani da su da tsawon lokacin shirye-shirye da wasikun da gidan rediyon kasar Sin ya samu dukkansu suna gaba a kan gidajen rediyon kasashen duniya 3 mafi girma.

A da, yawancin masu sauraronmu kun saurari shirye-shiryenmu ne ta gajeren zango. Amma a cikin wasu shekarun da suka wuce, irin wannna halin da ake ciki yana samun sauye-sauye a kai a kai.

Ran 27 ga watan Fabrairu na shekara ta 2006, wata muhimmiyar rana ce da ya kamata a tuna da ita a cikin tarihin watsa labaru ga kasashen waje na kasar Sin. A wannan rana, a birnin Nairobi na kasar Kenya, gidan rediyon FM a kan zango 91.9 da gidan rediyon kasar Sin ya kafa ya fara aiki.

Gidan rediyon FM a kan zango 91.9 na Nairobi gidan rediyo na FM ne na farko da gidan rediyon kasar Sin ya kafa a ketare. Lokacin da ake kaddamar da wannan rediyo, Mr. Wang Gennian, shugaban gidan rediyon kasar Sin ya shugabanci wata kungiyar wakilan gidan rediyon sun je kasar Kenya domin tabbatar da wannan lokaci mai matukar ma'anar a tarihi da idonsa. Gidan rediyo na FM da gidan rediyon kasar Sin ya kafa a birnin Nairobi na kasar Kenya ya cimma burin da dukkan mutanen gidan rediyon kasar Sin suke son cimmawa a cikin shekaru 65 da suka wuce. A cikin wadannan shekaru 65 da suka wuce, ko da yake, yawan harsunan da gidan rediyon kasar Sin yake amfani da su ya yi ta karuwa cikin sauri, amma hanyar watsa shirye-shiryenmu ba ta samu sauye-sauye sosai ba. Sabo da haka, bayan kaddamar da wannan gidan rediyon FM a birnin Nairobi, masu sauraro na kasar Kenya za su iya saurarar shirye-shiryenmu da sauki kwarai. Mr. Wang Gennian ya ce, "Nan da shekaru 5 masu zuwa, gidan rediyon kasar Sin zai kafa gidajen rediyo na FM ko na MW kimanin dari 1 a ketare. A sakamakon haka, masu sauraronmu da ke kasashen Asiya da Afirka da Latin Amurka da nahiyar Amurka ta arewa da Turai za su iya kama zangon gidan rediyon kasar Sin cikin sauki. A sa'i daya kuma, za mu kara kyautata ingancin shirye-shiryenmu. A sabili da haka, za mu kara mai da hankali kan yadda za a watsa shirye-shiryenmu masu dadin ji ga masu sauraronmu wadanda suke da ilmi da mukami a zaman al'umma. Muna fatan masu sauraronmu za su iya kara sani da fahimtar kasar Sin daga dukka fannoni bayan da suka saurari shirye-shiryenmu."

Jama'a masu sauraro, lokacin da yake kara mai da hankali kan yadda za a kara kyautata ingancin shirye-shirye da hanyar watsa su a kan rediyo, gidan rediyon kasar Sin yana kuma mai da hankali sosai wajen raya shafin Internet. Yanzu, idan ka shiga shafin Internet namu, wato CRI Online, za ka iya samun shirye-shiryenmu iri iri. Ya zuwa yanzu, yawan lokutan shirye-shiryen da muke sabuntawa a kowace rana ya riga ya kai sa'o'i fiye da 210. Mutane fiye da miliyan 8 daga duk fadin duniya suna shiga shafinmu na Internet na gidan rediyon kasar Sin a kowace rana. Bugu da kari kuma, a watan Yuli na shekarar bara, sashen shafin Internet na gidan rediyon kasar Sin ya kafa INET Radio, inda za a iya saurarar labarai da kide-kide da wakoki da shirin koyon harsuna da aka tsara da harsunan Sinanci da Jamusanci da Japanese. Yanzu masu leka shafinmu na Internet suna maraba da wannan INET Radio kwarai.

Mr. Ma Weigong, mataimakin babban edita na gidan rediyon kasar Sin kuma babban edita na shafin internet na CRI Online ya bayyana cewa, "Lokacin da muke ci gaba da raya shirye-shiryenmu da harsuna iri iri a kan shafinmu na internet, za mu kara mai da hankali wajen raya Blog da Podcast da harshen Sinanci har da harshen Turanci da Japananci da dai sauran harsuna. Sannan kuma, a wani lokacin da ya dace, za mu yi amfani da sabuwar fasahar zamani domin fara watsa shirye-shiryenmu na rediyo da samar da shirye-shiryen rediyo mai hoto ta hanyar sadarwa ta salula. Bugu da kari kuri kuma, za a fara aikinmu na koyar da harshen Sinanci a kan shafin Internet. Masu leka shafinmu na Internet za su iya koyon harshen Sinanci a kan shafinmu na Internet."

Jama'a masu sauraro, a nan gaba, gidan rediyon kasar Sin zai kara mai da hankali wajen neman bunkasuwa. Lokacin da yake tabo makomar gidan rediyon kasar Sin, Mr. Wang Gennian, shugaban gidan rediyon ya ce, "Burin da gidan rediyon kasar Sin zai cimma a nan gaba shi ne, zai zama wata kafar watsa labaru ce da ke hade da rediyon gargajiya da shafin Internet da kuma multimedia. Ta hanyoyin rediyo da shafin internet da rediyo mai hoto, za mu samar da labaru iri irin da ke shafar kasar Sin ga masu sauraronmu da masu karanta shafinmu na internet. Sabo da haka, ba ma kawai masu sauraronmu na kasashen waje za su iya kara sani da fahimtar kasar Sin ta shirye-shiryenmu ba, har ma masu sauraronmu na kasar Sin ma za su iya kara sanin kasashen duniya ta shirye-shiryenmu."

To, jama,a masu leka shafin Internet, kafin mu kawo karshen shirinmu na yau, bari mu maimaita tambayoyin. Na farko ita ce, yanzu gidan rediyon kasar Sin yana da ofisoshin wakilansa guda nawa a duk fadin duniya? Tambaya ta biyu ita ce, harsuna nawa yake amfani da su domin watsa shirye-shirye? Tambaya ta uku ita ce, a wace kasa ce gidan rediyon kasar Sin ya kafa wani rediyon FM na farko? Tambaya ta hudu ita ce, Yaya sunan shafin Internet na gidan rediyon kasar Sin? (Sanusi Chen)