Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-14 16:40:43    
Wata samfur wajen warware rikicin yankuna da ke tsakanin kasa da kasa

cri

Ran 12 ga wata a shiyyar da ke kusa da birnin New York a kasar Amurka, Olusegun Obasanjo, shugaban kasar Nijeriya, da takwaransa na kasar Cameroon, Paul Biya sun daddale wata yarjejeniya dangane da rikicin yankin tsibirin tekun Bakassi da ke tsakanin kasashen biyu.

An daddale wannan yarjrjrniya ne a cikin sulhuntawa da Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya yi. Bisa yarjejeniyar, kasar Nijeriya za ta janye dukan sojoji daga tsibirin tekun Bakassi a cikin kwanaki 60 masu zuwa, kuma za a gama aikin wucin gadi a cikin shekaru 2 nan gaba.

Tsawon iyakar da ke tsakanin kasashen Nijerya da Cameroon ya kai sama da kilomita 1680. Sakamakon matsalar iyakar kasa a lokacin mulkin mallaka na kasashen yamma, ana ka-ce-na ce tsakanin bangarorin Nijeriya da Cameroon game da iyakokin teku da yankunan kasa. Tsibirin Bakassi yana kudacin iyakar da ke tsakanin kasashen biyu, fadinsa ya kai muraba'in kilomita 665, ikon mallakarsa shi ne wata muhimmiyar matsalar da ke tsakanin bangarori biyu. A karshen shekaru 70 na karnin da ya wuce, an fara samun man fetur da gas a yankin ruwa da ke kusa da zirin, sabo da haka rikicin neman ikon mallakar tsibirin Bakassi da ke tsakanin kasashen Nijeriya da Cameroon ya yi ta kara tsanani. Tun daga shekarar 1993, sau da yawa kasashen biyu sun tayar da rikicin soja a wannan tsibirin.

A watan Maris na shekarar 1995, gwamnatin Cameroon ta gabatar da wannan gardama ga kotun duniya ta Hague, don yi hukunci. A watan Oktoba na shekarar 2002, kotun duniya ta Hague ta yi hukunci na karshe: wato za a ba da ikon mallakar tsibirin Bakassi ga kasar Cameroon, kuma ta bukaci kasar Nijeriya da ta janye sojoji da mayar da ikon mallaka ga kasar Cameroon kafin Watan Satumba na shekarar 2004. Nan da nan, shugaban kasar Cameroon ya bayar da wata sanarwa, inda ya nuna maraba ga hukuncin. Amma, gwamnatin kasar Nijeriya ta bayar da sanarwar cewa, ta ki yarda da wannan hukunci, a sa'i daya kuma ta bayyana cewa, za ta ci gaba da kiyaye kyakkyawar dangantakar makwabtaka da ke tsakanin kasashen Nijeriya da Cameroon, domin warware gardamar zirin nan cikin lumana ta hanyar siyasa. A watan Nuwamba na shekarar 2002 a Geneva, bisa gayyatar da Kofi Annan, babban sakataren M.D.D. ya yi musu, shugabannin kasashen biyu sun yi tattaunawa, da kuma bayar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka bayyana cewa, za su warware ka-ce-na-ce game da iyakar kasa ta hanyar lumana. Gaba daya bangarorin biyu suka yarda da kafa kwamitin aiki da cikawa, domin aiwatar da hukuncin da kotun duniya ta yi. A watan Disamba na shekarar 2002 a kasar Cameroon, kwamitin nan ya shirya taro na karo na farko, kuma ya bayar da wani rahoto, wato kafa wata hadaddiyar hukumar tantancewa da ke karkashin shugabancin kwamitin, domin yi bincike kan shiyoyyin da ke da nasaba da iyakar da ke tsakanin kasashen biyu, a sa'i daya kuma an kafa wani kwamiti mai kula da aikin shata iyakar kasa. Bayan haka kuma, a cikin kokarin da kwamitin ya yi, kasashen Nijeriya da Cameroon sun kara samun ci gaba wajen janye sojoji, da mika ikon mallaka, da binciken iyakar kasa a shiyyar da ake gardama a kai, haka kuma bi da bi aka warware ka-ce-na-ce game da iyakar kasashen biyu.

Manazarta suna ganin cewa, kasashen Nijeriya da Cameroon sun warware gardamar nan cikin lumana, wannan ya nuna samfur ga sauran kasashe masu kasance da rikici dangane da matsalar iyakar kasa, haka kuma ana ganin muhimmin amfani na matakan da bangarori daban daban suka dauka wajen warware gardama.

Ran 12 ga wata, Mr. Obasanjo, shugaban kasar Nijeriya ya bayyana cewa, yarjejeniyar da bangarorin Nijeriya da Cameroon suka daddale ita ce wani muhimmin sakamako da aka samu wajen rigakafin rikici, tana da ma'ana sosai, kuma ta gabatar da abin koyi ga Afrika da kuma dukan duniya, domin warware rikici kamar haka.