Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-14 15:00:08    
Kungiyar WTO ta ce yawancin kasashen duniya ba su iya tabbatar da lafiyar jinin da suke bayarwa ba

cri

Ran 12 ga watan Yuni, kafin ranar ba da jini na ran 14 ga wata, kungiyar WTO ta bayar da sanarwa cewa, yanzu jinin da yawancin kasashen suke yi amfani ba dukansu su zo daga jinin da aka ba da na kyuata ba.

Daidai bisa wannan yanayi ne, aka samo wata hanya mai amfani, wato kamata ya yi a ba da ilmi ga kowa da kowa a fannin riga-kafin ciwon kan-jiki da kuma kara fadakar da mutane a fannin yaki da irin wannan mugun ciwo. Gwamnatin kasar Sin ita ma tana mai da hankali sosai kan wannan babban aiki. To, a cikin shirinmu na yau, za mu dan gutsura muku wani bayani kan yadda ake fadakar da manoma wadanda suke yin aikin lebura a birane na kasar a fannin riga-kafin ciwon kan-jiki.

A halin yanzu, akwai manoma da yawansu ya kai miliyan dari da ashirin dake yin aikin lebura a birane na kasar Sin. Matsayin ilmi na wadannan manoma ya yi kasa-kasa. Saboda haka, ba su san me nene ciwon kan-jiki ba; kuma kashi 65 cikin kashi 100 na wadannan manoma, samari ne dake da shekaru 20 zuwa 40 da haihuwa; dadin dadawa, mutane ba kadan ba daga cikinsu sukan rabu da mazajensu ko matansu yayin da suke yin aikin lebura a birane. Don haka ne kuwa, tunaninsu a fannin jima'I ya sauya, wato ke nan sukan gudanar da harkokin jima'I marasa da'a.

Ban da wannan kuma, wadannan manoma sukan malala zuwa wurare dabam daban bisa bukatarsu wajen samun aikin yi. Sakamakon haka, da zarar sun kamu da kwayoyin cutar kan-jiki masu lambar HIV, to kuwa mai yiwuwa ne irin wadannan kwayoyi za su kara yaduwa ko'ina.

Bisa wannan dalili dai, gwamnatin kasar Sin tana kokari matuka wajen fadakar da manoma wadanda suke yin aikin lebura a birane a fannin samun ilmin riga-kafin ciwon kan-jiki. Ga hukumomin gwamnati da kuma kungiyoyin jama'a masu yawan gaske da abun ya shafa sukan gudanar da ayyuka iri dabam daban, wato sukan yi farfaganda kan riga-kafin ciwon kan-jiki a wuraren da mutane ke cunkushe har ma a kan hanyoyin zirga-zirga.

Jirgin kasa, saboda hanyar zirga-zirga ce da manoma suka fi daukarsa zuwa birane domin yin aikin lebura. Saboda haka, ana kara mai da hankali sosai kan aikin fadakar da mutane a fannin samun ilmin riga-kafin ciwon kanjamau. A kwanakin baya ba da dadewa ba, wani fasinja mai suna Iglisias daga kasar Spain ya bayyana ra'ayinsa cike da farin ciki a gaban wakilin redionmu lokacin da yake duba yadda mutane masu sa kai daga kungiyar agaji ta Red Cross suke rarraba takardun farfaganda, inda ya fadi, cewa " A kasarmu kuwa nakan ga irin irin wannan harka mai kyau, wadda ta jawo fa'ida ga mutane da dama".

Madam Jiang Yiman, mataimakiyar shugaban kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Sin ta fada ,cewa a ganina, kamata ya yi a sa lura sosai da manoman da sukan malala zuwa birane domin yin aikin lebura lokacin da ake yin farfaganda kan yadda za a yi riga-kafin ciwon kanjamau.

Ban da wadannan kuma, sassan da abun ya shafa na ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin takan manna takardun farfaganda a kan bangunan gidaje na kauyukan duk kasar.

Kwanakin baya ba da jimawa ba, gwamnatin kasar Sin ta kuma soma gudanar da wata harkar ilmantarwa kan aikin riga-kagin ciwon kanjamau a cikin dukkan manoman da suke yin aikin lebura a biranen kasar.

Gwamnatin kasar Sin tana fatan kashi 65 cikin 100 na manoman dake yin aikin lebura a birane za su iya fahimtar ilmin riga-kafin ciwon kan-jiki daga dukan fannoni a karshen wannan shekara ta wannan hanyar farfaganda