A ran 10 ga watan nan da asuba, agogon Beijing, an yi bikin bude gasar cin kofin duniya ta 18 ta wasan kwallon kafa a birnin Munich dake kudancin kasar Jamus. A ranar farko ta gasar, kasar Jamus ta ci ta Costa Rica da ci hudu da biyu. Kungiyoyin kasashe 32 na duniya sun shiga gasar. Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ba ta samu iznin shiga wannan gasa ba, amma dimbin ma'abutan kwallon kafa na kasar Sin suna cike da farin da ciki da kallon gasanni masu ban sha'awa ta T.V ;
A gun gagarumar gasar samun kyaututtuka ta wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasa da kasa da aka yi ran 11 ga watan nan a kasar Burtaniya, shahararren dan wasa mai suna Asafa Powell daga kasar Jamaica ya cimma matsayi na daya a duniya a gun wasan gudu na gajeren zango na mita 100 na maza da dakika 9 da digo 77, wanda ya kago a shekarar 2005 a Aden.
A gun gasar wasan kwallon tenis da aka yi a ran 11 ga watan nan a kasar Fransa, ' yan wasa su Zhenjie da Yanzi na kasar Sin sun shiga jerin kungiyoyi hudu masu karfi a gun wasa tsakanin mata bibbiyu, wato ke nan sun samu sakamako mafi kyau a tarihin gasar wasan tenis da aka saba yi a kasar Faransa.
Ban da wannan kuma, sannannen dan wasa mai suna Rafael Nadal daga kasar Spain ya lallasa abokin karonsa mai suna Roger Federer daga kasar Swiss da ci uku da daya, wato ke nan ya sake samun lambar zinariya a gun wannan gasa ; kuma ' yar wasa mai suna Justine Henin daga kasar Belgium ta zama zakara a gun gasar.
A gun gasar karshe ta wasan kwallon boli ta mata da aka yi a ran 11 ga watan nan, kungiyar kasar Brazil ta lashe ta kasar Sin da ci uku da biyu.( Sani Wang )
|