Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-13 17:21:58    
Ana mai da hankali sosai ga kare tsarin tarihi na birnin Shanghai

cri
A kwanakin baya, akwai kafofin watsa labaru wadanda suka nuna damuwarsu ga tsoffafin gine-ginen birnin Shanghai da za a bata, yayin da ake gina unguwar babban bikin baje koli na duniya a birnin Shanghai. A kan wannan, wakilinmu ya sami labarin cewa, yanzu an riga an kaurar da duk mazauna daga unguwar nan, sa'an nan kuma an kare tsoffafin gine gine nagartattu da kyau kwarai.

Da ma Madam Wang Guimei da 'yan iyalinta biyu sun yi zamansu a wani wuri da ke gabar yammacin kogin Huangpu. Gidansu yana cikin unguwar da za a shirya babban bikin baje koli na duniya, sabo da haka an rushe tsohon karamin gidansu, kafin haka an kaurar da su zuwa wani wuri mai nisan sama da kilomita 10 daga cibiyar birnin Shanghai, suna sami wani sabon gida mai fadin muraba'in mita 80. Madam Wang ta gaya wa wakilinmu cewa,"kudin da na kashe don sayen wannan sabon gida mai kyau duk bisa aljihun gwamnati ne. Amma na kashe kudi kalilan wajen kayatar da gidana. Manufar da gwamnatin ke bi dangane da gina sabuwar unguwar babban bikin baje koli na duniya tana da kyau kwarai."

Abin da ya sha banban da na sauran bukukuwan baje koli na duniya da aka taba shiryawa shi ne yawancinsu a karkarar birane ne, an zabi wata unguwa da ke cibiyar birnin Shanghai don shirya babban bikin baje koli na duniya a shekarar 2010. Fadin unguwar ya kai muraba'in kilomita 5. Yawan iyalan mazauna daidai da na Madam Wang wadanda wajibi ne a kaurar da su zuwa sauran wurare ya wuce dubu 18. Bisa binciken da aka yi kan wadannan mazauna, an gano cewa, yawancinsu sun gamsu da sabbin wurare da suke zama a yanzu duk domin manufar nuna gatanci da gwamnati ta aiwatar.

Malam Mao Jialiang, shugaban ofishin kula da harkokin tsarin birnin Shanghai kuma daya daga cikin masu tsara fasalin unguwar babban bikin baje koli na duniya ya bayyana cewa, an mai da hankali sosai ga kare tsarin tarihi da tsoffafin gine-gine na birnin Shanghai, yayin da ake tsara kasafin unguwar. Duk fadin irin gine-ginen da za a kare su ya wuce murabba'in mita dubu 400. Ya bayyana cewa,"kara kokari wajen kare tsarin tarihin wani birni ta zama wata alama ce ga al'adun birnin nan, kuma wata babbar ka'ida ce da muke bi wajen shirya babban bikin baje koli na duniya. Gwamnatin birnin Shanghai tana yin aikin gina wannan unguwa ne ta hanyar kafa doka da tsari da abin ya shafa don kare tsofaffin gine gine da sauransu, sa'an nan kuma tana nuna himma da kwazo wajen gano hanyar da za a bi wajen kare tsarin tarihi na birnin Shanghai, wato birni mai girma da ba safai a kan same irinsa ba a duniya. "

Yau da shekaru sama da 100 ke nan da gina birnin Shanghai. Duk fadin tsoffafin gine-gine nagartattu da aka yi a birnin Shanghai ya wuce muraba'in mita miliyan 4. Daga cikinsu akwai gine-gine irin na gargajiyar kasar Sin da na Turai da sauran kasashe. Bisa matsayinsa na shahararren birnin al'adu na kasar Sin, a shekarar 2003, birnin Shanghai ya mayar da unguwoyin cibiyarsa guda 12 don su zama unguwoyin da za a kare su sosai.

Yayin da wakilin gidan rediyonmu ya kai ziyara ga Malam Yang Xiong, mataimakin magajin gari na Shanghai don jinta bakinsa, sai ya bayyana cewa,"ko da yake wajibi ne gwamnati ta taka muhimmiyar rawa wajen gina unguwar babban bikin baje koli na duniya, amma kare tsarin tarihin birnin ba aikin gwamnati kadai ba ne, kuma nauyi ne da ke bisa wuyan bangarorin jama'a daban daban. Tsoffafin gine-gine da za a kare su dukiyoyi ne masu daraja da aka bari ga duk jama'a. Idan aikinmu na gina unguwar nan ya shafi wadannan tsoffafin gine-gine masu kyau, to, dole ne mu yi rangwame a kansu. Ya kamata, gwamantin birnin Shanghai ta aiwatar da tsarin kare su a tsanake, ta yadda za a kare tsarin tarihi na birnin da kyau. (Halilu)