Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-13 16:06:12    
Baradei ya yi kira ga kasar Iran da ta gama kai da kasashen duniya domin warware matsalar nukiliya ta kasar ta hanyar zaman lafiya

cri

A ran 12 ga wata, babban daraktan hukumar makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA a takaice Mohamed El-Baradei ya sake yin kira ga kasar Iran da ta gama kai da kasashen duniya domin warware matsalar nukiliya ta kasar ta hanyar zaman lafiya.

Mr Baradei ya yi wannan bayani ne a gun taron majalisar kungiyar IAEA da aka shirya a birnin Vienna a ran nan. Ya ce, ya yi imani cewa, hanyar warware matsala ita ce yin shawarwari da fahimtar juna da ke tsakanin bangarori daban daban. Zai kara sa kaimi ga kasar Iran da ta gama kai domin warware matsalar nukiliya ta kasar. A sa'i daya kuma Mr Baradei ya yi maraba da kokarin da sassan da abin ya shafa suke yi domin warwari matsalar ta hanyar diplomasiyya.(Danladi)