Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-12 15:23:41    
Halayen mutanen kasar Bulgaria masu ban dariya sosai

cri
Jama'a masu karatu, yanzu ga shirinmu na filin yawon duniya; ga wani labarin da wakilin kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, halayen mutanen kasar Bulgaria suna da sha'awa sosai, musamman wadansu tsofaffi suna iya bayyana tatsuniyoyi iri iri kuma masu ban dariya sosai.

Wani gari mai suna Bugario dake karkashin wani babban tudu, wurin nan ya yi shahara a duk kasar Bulgaria, domin mutane na garin nan sun iya bada tatsuniyoyi iri daban daban kuma masu ban dariya. An ce, wani tsoho ya kago wannan gari wato karamin birnin. A karkashin wani babban ice, wani tsoho ya kafa karamin kantin sayar da kayayyakin gona, domin halinsa mai ban sha'awa, haka ne yana ta kara jawo sha'awar mutanen da suka zo daga nesa, a karshe dai wani kauye ya kafu, A wurin nan mutane sun fara yi kananan sana'o'I iri iri, misali yin sake sake da yin rina da yin gyare gyare ga wadansu kayayyakin noma.Ban da haka mutane na wurin nan suna iya yin cinikin kayayyakin gona da kyau.

A kwana a tashi, wannan gari yana nan yana girma, har ya zama wani karamin birni da ya shahara a duk kasa wajen yin kananan sana'o'I da yin ciniki. Mutane na wannan wuri suna dade suna fama da wahala da yawa wajen neman samu arziki, a karshe dai ko da yake sun yi arziki, amma suna zaman rayuwa cikin halin tsimin kudi sosai. Wato suna da halin kirki, kuma suna iya kawo wa mutane abubuwa masu ban dariya, sai mutane na wannan kasar suna son halayen mutanen wurin nan sosai.

Mutane na wannan gari sun yi tattalin zaman rayuwa sosai, kuma a kan sassa daban daban ne an iya gani halinsu na yin tsimin kudi sosai, Misali, dakunan da suka gina ba masu fadi ba, musamman don yin tsimin kayayyakin gine gine.

Karin magana na mutanen wurin nan shi ne "akwai dariya akwai duniya", wato mutane na wannan gari sun mai da bayyana abubuwa masu ban dariya kaman wani babban sha'aninsu. Tun daga shekara ta l973 na karnin da ya shige, a garin nan, akan shirya baje kolin fasahar nuna abubuwa masu ban dariya na duniya a kowace shekara, ta haka ne akan jawo sha'awar mutane na kasashe daban daban da sukan zowa daga wurare daban daban na duk duniya.Ban da haka kuma,an kafa dakin nune nunen fasahar bayyana abubuwa masu ban dariya da sha'awa sosai, daga sinima da wake wake da zanen da aka zana da sassakakkun dawatsu iri iri, dukkansu sun iya kawo ban dari ga mutane, An ce, makasudin yin baje kolin fasahar nuna ban dariya shi ne don sa mutane daga shekarunsu sun kai 5 zuwa l00 da haihuwa su yi murmushi da yin dariya sosai da sosai.

Yanzu, wannan dakin yin baje koli na fasahar nuna abubuwa masu ban dariya ya buga wani litaffi don tattara abubuwa masu ban dariya fiye da dari, har an fassara wannan litaffi da harsuna iri iri fiye da 20, kuma kasashe da yawa sun yi odar neman sayen wannan litaffi mai ban sha'awa.

A kowace shekara, a nan akan shirya shagugula masu ban sha'awa, mutane na garin nan sukan saye da tufaffi iri iri masu jawo hankunan mutane, tsofaffi da yara , kuma samarin maza da mata sukan yi wake wake da raye raye, kai a nan mutane suna jin dadin zamansu sosai da sosai. (Dije)