 Wakilin Kamfanin dillancin labarum Xinhua na kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 9 ga watan nan , za a bude wasan Gasar kwallon kafa ta duniya ta 2006 a kasar Jamus . Ko da ya ke Kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ba za ta shiga wannan wasa ba , amma Masu sha'awar kwallon kafa na Kasar Sin suna mai da hankali sosai kan wasan .
Agogon Kasar Sin da na lasar Jamus suna da bambancin awa 6 , amma galibin masu sha'awar kwallon kafa za su duba gasa ta hanyar talabijin kai-tsaye . A cikin kungiyoyin da suke goyon baya akwai kungiyar Brazzil da Italy da Spain da Argentina da sauransu .
Kwanan baya yayin da Firayin minista Wen Jiabao na kasar Sin ya gana da Madam Angela Merkel , takwararsa ta kasar Jamus , ya bayyana cewa , shi ma mai sha'awar kwallon kafa ne . (Ado)
|