Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-08 20:35:59    
Liu Xiang ya sake cin nasara

cri
Zakarar taron wasannin Olympic na Athens Liu Xiang ya ji rauni ba zato ba tsammani a watan Fabrairu na shekarar da muke ciki, wannan ya taba jawo hankulan mutane da yawa. Bayan da ya yi hutu a tsanake, Liu Xiang ya sake gwada gwanintarsa lami lafiya, sau biyu ne a jere ya ci nasara a cikin gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 tsakanin maza ta gasar ba da babbar kyauta da Hadaddiyar Kungiyar Wasannin Guje-guje da Tsalle-tsalle ta Duniya wato IAAF ta shirya. A cikin bayanin musamman da za mu ci gaba da karanta muku, za mu dan gutsura muku da halin da Liu Xiang yake ciki a yanzu.

Mutane sun mayar da Liu Xiang kamar wani saurayi mai karfi kuma wanda ba ya son a lashe shi. Bayan da ya zama zakara a cikin taron wasannin Olympic na Athens, ya zama daya daga cikin taurarin wasannin motsa jiki da 'yan kasar Sin suke fi sonsu. Amma a lokacin da ya himmantu ga share fage ga sabbin gasanni, Liu Xiang ya jikata ba zato ba tsammani a watan Fabrairu na wannan shekara, ta haka ya bar filin wasa ya dakatar da horo a cikin dogon lokaci, har ma raunin da ya ji ya tilasta masa ya yi watsi da gasar fid da gwani ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya da aka yi a cikin dakin wasa a birnin Moscow a watan Maris na bana.

Mutanen kasar Sin sun zura ido kan Liu Xiang da ya sake shiga gasar gudun ketare shinge mai tsawon mita 110, a karshe dai sun sami labarin cewa, zai sake shiga gasanni a watan Mayu. Bayan da aka warkar da shi, Liu Xiang ya gwada gwanintarsa lami lafiya, bi da bi ne ya zama zakara a cikin gasannin gudun ketare shinge mai tsawon mita 110 da kungiyar IAAF ta shirya a biranen Osaka na kasar Japan da Eugene na kasar Amurka. Abin da aka lura shi ne, a cikin gasar da aka yi a Eugene, Liu Xiang ya lashe sahararrun 'yan wasa Ladji Doucoure, dan kasar Faransa da kuma Allen Johnson, dan kasar Amurka, wannan ne karo na farko da Liu Xiang ya ci nasara a cikin gasar da dukansu uku suka shiga. Ko da yake cin nasara ya faranta ransa, amma Liu Xiang yana ganin cewa, dan gasa mafi karfi da zai lashe shi a cikin gasa shi ne kansa, yana bukatar lashe kansa a cikin ko wace gasa. Ya ce

'idan an ambaci 'yan gasa, ina da su da yawa daga kasashen Amurka da Faransa da sauran kasashen. Amma ina tsammanin cewa, dan gasa mafi karfi shi ne ni kaina, zan yi iyakacin kokarina kamar yadda na kan yi a lokacin horo.'

Saboda fasahohin da ya samu daga gasannin duniya da ya shiga a shekarun nan da suka wuce, da kuma raunin da ya ji a wannan gami, Liu Xiang ya girma, ya iya kyautata hankalinsa a duk lokacin da ya gamu da matsala ko a'a, mai yiwuw ne wannan daya daga cikin muhimman dalilan da suka sa ya rika samun maki mai kyau.

Saboda babbar nasarar da ya ci a cikin taron wasannin Olympic na Athens, ba ma rukunin wasannin motsa jiki na duniya sun canja ra'ayinsa kan wasannin guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin kawai ba, har ma Liu Xiang ya sami girmama da yabo. Sahararren dan wasan kasar Amurka Allen Johnson ya yi magana kan wannan dan wasan kasar Sin mai baya da shi, ya ce,

'yaya ra'ayina kan Liu Xiang? To, ya iya gudu cikin sauri, shi ne tauraro ne da yake tashi zuwa sararin samaniya, amma ni tsohon tauraro ne da nake faduwa sannu a hankali.'

Nan gaba, Liu Xiang zai shiga gasar ba da babbar kyauta da kungiyar IAAF za ta shirya a Lausanne da kuma gasar cin kofin duniya ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle da sauran gasanni a jere, inda zai ci gaba da yin takara da Doucoure da Johnson, kuma takarar da ke tsakaninsu za ta ci gaba da kasancewa har zuwa taron wasannin Olympic na Beijing na shekarar 2008. Liu Xiang ya san ainihin makasudinsa sosai, wato taron wasannin Olympic da za a yi a Beijing a shekarar 2008. Karfinsa da kuma share fage da ya yi a fanin hankali sun zama tabbaci na gare shi a fannin ci gaba da cin nasara, babban malamin wasa na kungiyar wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin Mr. Feng Shuyong yana da karfin gwiwa sosai kan makomar Liu Xiang, ya ce

'na yi imanin cewa, Liu Xiang yana da karfi da yawa da bai yi amfani da shi ba. Zai iya kyautata abubuwa da yawa, na tabbatar da cewa, yana da karfin da bai yi amfani da shi ba.'