Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-08 17:04:22    
Gwamnatin kasar Sin na kokarin ingiza hadin gwiwa tare da kasashen ketare a fannin tattalin arziki yayin da take yin amfani da jarin waje kamar yadda ya kamata

cri

Yau Alhamis, a nan Beijing, mataimakiyar ministan kasuwanci na kasar Sin Madam Ma Xiuhong ta bayyana, cewa yanzu gwamnatin kasar Sin tana nan tana ta yin kwaskwarimar tsarin sana'o'I da aka kafa bisa jarin ' yan kasuwa daga kasashen ketare. Ban da wannan kuma yayin da take bunkasa sana'ar kere-kere na zamani, tana kuma yin yunkurin daukaka ci gaban cinikayya ta hidima da kuma nuna himma da kwazo wajen yin hadin gwiwa tare da kasashen ketare a fannin tattalin arziki har da bada jagoranci ga kamfanoni da masana'antu na kasar Sin don su zuba jari a kasashen ketare.

Shigo da jari daga kasashen ketare, wani muhimmin abu ne dake cikin manufar gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da gwamnatin kasar Sin take aiwatarwa, kuma kyakkyawar muhallin zuba jari ya jawo hankulan ' yan kasuwa masu zuba jari na duk duniya. Ya zuwa karshen shekarar bara, masu zuba jari daga kasashe da jihohi da yawansu ya kai kusan 200 sun kafa kamfanoni da masana'antu masu jarin gefe daya kacal ko masu jarin hadin gwiwa wadanda yawansu ya zarce 500,000. Yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da shi a zahiri ya wuce dola biliyan 600.

A gun wani taron yada labarai da aka shirya yau a nan Beijing, mataimakiyar minista Madam Ma Xiuhong ta fadi, cewa lokacin da gwamnatin kasar Sin take dukufa kan shigo da jarin waje don bunkasa sana'ar kere-kere, tana kuma nuna himma da kwazo wajen kyautata tsarin harkokin yin amfani da jarin waje. A cikin tsarin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'umma na shekaru biyar masu zuwa da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da shi kwanakin baya ba da dadewa ba, an bayyana a fili, cewa : ' Nan da shekaru biyar masu zuwa, za mu kara kyautata tsarin sana'o'in da aka kafa bisa jarin ' yan kasuwa daga kasashen ketare, kuma za mu sa kaimi ga ' yan kasuwan wajen zuba jari don kafa kamfanoni da masana'antu na zamani, da cibiyoyin nazari da kuma kamfanonin kawo albarka masu ci gaba ; A sa'i daya kuma za mu himmantar da su wajen zuba jari a fannin cinikayyar hidima domin sanya matukar karfi wajen ingiza sana'ar hidima ta zamani ta kasarmu.'

A yayin da gwamnatin kasar Sin take ci gaba da kara bude kofa ga kasashen waje da kuma shigo da jari daga ketare, tana kuma himmantuwa wajen sa kaimi ga kamfanoni da masana'antu masu karfi don su shiga cikin harkokin hadin gwiwa tare da kasashen ketare a fannin tattalin arziki da cinikayya domin neman sabuwar kyakkyawar damar samun yalwatuwa. Ya zuwa karshen shekarar bara, yawan jarin da kamfanoni da masana'antu na kasar Sin suka zuba kai tsaye a kasashen ketare ya riga ya dara dola biliyan hamsin da daya da miliyan dari bakwai ; A sa'i daya kuma, kasar Sin ta samu babban ci gaba wajen ayyuka iri daban daban na taimaka wa kasashen ketare.

A gun taron yada labarai da aka shirya a yau, Madam Ma Xiuhong ta jaddada, cewa sa kaimi ga kamfanoni da masana'antu na kasar Sin don su shiga cikin harkokin bunkasa tattalin arziki na kasa da kasa, wani muhimmin aiki ne da gwamnatin kasar Sin take yi. Ta furta, cewa :'Har kullum mukan sa kaimi ga kamfanoni da masana'antu na kasar Sin don su zuba jari a kasashen ketare, ba ma kawai a kasashe masu tasowa ba, har ma a kasashe masu sukuni'.

Madam Ma ta kuma bayyana, cewa a 'yan shekarun baya, gwamnatin kasar Sin ta riga ta dauki matakan gyare-gyare da dama, ta yadda za ta kara taka muhimmiyar rawa cikin yunkurin bunkasa tattalin arzikin duk duniya.( Sani Wang )