Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-07 19:37:50    
A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku da wani shirin "Ni da CRI"

cri
Jama'a masu sauraro, shekarar da muke ciki shekara ce ta cika shekaru 65 da kafa rediyon kasar Sin wato CRI. Bisa matsayin farko na gidan rediyon watsa labaru ga kasashen waje , yaya aka kafa rediyon CRI? Wace irin hanyar take bi wajen samun bunkasuwarsa? A cikin shirinmu na yau, za mu gabatar muku wasu abubuwa dangane da tarihin somawar kafa sa .

Kafin shirye-shiryenmu na yau, za mu gabatar da tambayoyi guda biyu, na farko shi ne, wane ne ya soma karanta labaru a karo na farko a gidan rediyonmu? Na biyu, a watan Afril na shekarar 1950, Me ne ne sunan rediyonmu ?

A farkon shekaru 40 na karni na 20, kasar Sin tana kasancewa cikin zamanin yin dagiya da maharan sojanci na kasar Japan. A cikin zamanin can na yin yake-yake, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da dakarun da ke karkashin jagorancinta sun zama karfin ginshiki na yin dagiya da harin Japan. Don yin farfagandar yin dagiya da harin Japan, a birnin Yan'an da ke arewa maso yammacin kasar Sin, wato inda kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke zama, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kafa gidan rediyon Xinhua na Yan'an don bayyana halin da ake ciki a gida da waje na zamanin can da kuma kirayi rukunoni daban daban na zamantakewar al'umma na gida da na waje don yin dagiya da Japan cikin hadin guiwa. A ran 3 ga watan Disamba na shekarar 1941, gidan rediyonmu ya soma watsa labaru da harshen Japannaci a karo na farko, sunan rediyon shi ne "XHCR" , masu sauraron gidan rediyonmu su ne sojojin Japan masu kai wa kasar Sin hari, wato maharan Japan da ke zama a kasar Sin, sunan mai karanta labarai na farko ita ce marigayiya mai kin hari na kasar Japan Hara Kiyoshi. Kodayake dakin daukar murya na wancan zamani wani rami ne mai sauki da aka haka a tudai, kuma karfin injin watsa labaru na da watt 300 kawai, amma daga ranar , kasar Sin ta soma watsa labaru da harshen waje zuwa kasashen waje. Sa'anan kuma, an tsai da cewa, ran 3 ga watan Disamba na shekarar 1941 rana ce ta soma sha'anin kasar Sin na watsa labaru ga kasashen waje .

Mr Lu Rufu , bashinne da ke zama a kasashen waje kuma ya koma kasar Sin daga kasar Japan a shekaru 50 na karni na 20, ya yi aikin watsa labaru da harshen Japan cikin shekaru da yawa, ya san abubuwa da yawa dangane da yadda aka soma watsa labaru da harshen Japannanci a wancan zamani. Yanzu yana kusan cika shekaru 70 da haihuwa, ya bayyana cewa, Mai karanta labaru da harshen Japannanci Hara Kiyoshi ta karanta labaru a cikin ramin da aka haka a kan tudai na birnin Yan'an , muryarta ta zama babban mukamin da ke murkushe sojojin Japan a cikin yakin kin harin Japan.

A wancan zamani, Hara Kiyoshi ta yi amfani da muryarta don fadakar da mutanen Japan halin gaskiya na yake-yake da kuma wane bangare na da gaskiya, tana da karfin shawo kan sojojin Japan, kuma mutane da yawa sun sha tasirinta. Sa'anan kuma, kwararru da yawa na kasar Japan sun yi aiki a gidan rediyonmu , kusan dukansu sojoji ne na kasar Japan, wasunsu su da kansu sun ba da kai ga kasar Sin a cikin yakin, wasunsu sun gudu zuwa bangaren kasar Sin a asirce. Malamina sunansa Michiyuki Ogi shi ne wani sojan Japan, amma yana aikin watsa labaru ga kasar Japan a kasar Sin.

A shekarar 1946 da samun nasarar kin harin Japan, jam'iyyar Kuomintang da ke taba yin hadin guiwa da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a cikin yakin kin harin Japan ta ki kafa hadadiyyar gwamnati tare da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ta kai farmakin soja ga jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin , ta yi hakilon banza na kafa gwamnati ta kama karya, daga nan, jam'iyyar kwamins ta kasar Sin ta yi jagorancin jama'a don yin gwagwarmar neman yancin kai ta hanyar dimokuradiya. Bisa bunkasuwar halin da ake ciki na yin yake-yake, Gidan rediyon Xinhau na birnin yan'an yana watsa labaru yana kaurawa, sai a farkon shekarar 1947 ya sauka gundumar She na lardin Hebai da ke kusa da birnin Beijing, a watan Satumba na wannan shekarar, gidan rediyon Xinhua na birnin Yan'an ya soma watsa labaru da harshen Ingilish.

A lokacin soma karanta labaru da harshen Ingilish, karfin injunan watsa labaru ya riga ya kai kilowatt goma, an iya saurarar shirye-shiryenmu sosai da sosai a kasashen da ke kudancin Asiya da na kudu maso gabashin Asiya da na sauran kasashen Asiya, in yanayin sararin samaniya ya yi kyau, to an iya saurararmu a kasashen Turai da arewacin nahiyar Amurka da sauran wurare. Ta hanyar shirye-shiryenmu, kasashen waje sun iya samun labarun gaskiya da suka faru a kasar Sin.

Jama'a masu sauraro, a shekarar 1949, Jamhuriyar jama'ar Sin ta kafu, saboda haka gidan Rediyon Xinhua na birnin Yan'an shi ma ya kaura zuwa birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, shi ya sa an sauya sunansa da cewa "Rediyon Xinhua na Peking". Abun da kuke saurara yanzu shi ne shirinmu na wancan lokacin da Rediyon Xinhua na Peking ya watsa a gun babban bikin kafuwar sabuwar kasar Sin a ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, duk domin sanar wa duk duniya haihuwar Jamhuriyar jama'ar Sin.

Bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, cikin himma da kwazo ne gidan Rediyo kasar Sin ya bayyana wa kasashe daban daban na duniya manufofi da ka'idoji na gwamnatin kasar Sin da bunkasuwa da sauyawa da kasar Sin ta samu wajen siyasa da tattalin arziki da fannoni daban daban na zamantakewar al'umma da kuma ma'amala da hadin guiwa da ke tsakanin kasar Sin da kasashe daban daban na duniya, ya zama gadar da ke kara fahimta da zumunci a tsakanin jama'ar Sin da jama'ar kasashe daban daban, a lokacin aiwatar da dawainiyar tarihin, sha'anin watsa labaru ga kasashen waje shi ma ya sami ci gaba sosai, musamman ma wajen watsa labaru ta hanyar yin amfnai da harsunan waje, ya kara sabbin harsuna da yawa bisa tushen watsa labaru da harsunan waje guda biyu wato Japannanci da Ingilish da yaren wurare daban daba na kasar Sin guda uku kawai.

A shekarar 1950, an soma watsa labaru ga kasashen waje da sunan gidan rediyonmu cewa "Radio Peking" cikin Ingilish, abun da kuke saurara shi ne sunan nan da aka karanta, kidan da aka sanya shi ne kida mai suna Dongfanghong wanda kusan kowane mutum na kasar Sin ya iya rerawa, yana da halayen zamanin can sosai. A watan da aka soma yin amfani da sunan nan, don bayyana wa jama'ar shiyyar kudu maso gabashin Asiya halin da sabuwar kasar Sin take ciki da manufar diplomasiya ta yin lumana cikin mulkin kai ba tare da tsangwama ba, a daidai wancan lokacin, gidan rediyon Peking ya soma watsa labaru da harsuna Vitnam da Thailand da Indonesiya da Myamma don bayyana wa jama'ar kasashen da ke kudu maso gabashin Asiya fasahohin da kasar Sin ta samu wajen yin juyin juya hali da kuma himmantar da su wajen neman yancin al'ummarsu.

Sa'anan kuma, gidan rediyo Peking shi ma ya soma watsa labaru da harsunan hausa da Parisa da Larabaci da Swahili da Spain da dai saruansu don bayyana wa kasashen Larabawa da na Afrika kasar Sin mai mulkin gurguzu da kuma kara dankon zumunci a tsakanin jama'ar Sin da jama'ar kasashe masu tasowa.

Jama'a masu sauraro, a shekarar 1978, bisa albarkacin budewar kasashen waje kofa a kasar Sin, sha'anin watsa labaru ga kasashen waje na kasar Sin shi ma ya shiga sabon zamanin samun bunkasuwa. A cikin shirinmu na nan gaba, za mu yi maraba da ku don saurarar bayani na biyu dangane da gasar da muka shirya muku,

Yanzu, za mu sake maimaita tambayoyi guda biyu da muka gabatar muku, wane ne ya soma karanta labaru a karo na farko a gidan rediyonmu? Na biyu, a watan Afril na shekarar 1950, Me ne ne sunan rediyonmu ?

In ka aiko mana wasika, to za ka iya rubuta adireshinmu kamar haka: Lagos Bureau

China radiyo International

P.O.Box 7210 Victoria Island

Lagos

Nigeriya

Ko ta hanyar internet:

Hausa @ cri.com.cn