Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-07 19:35:11    
Wata zabiya ta kungiyar wake-wake da raye-raya ta mahakar kwal ta kasar Sin mai suna Wang Feifei

cri

Wang Feifei zabiya ce ta mahakar kwal ta kasar Sin. Muryarta na da dadin ji sosai. Ita ce zabiyar da ke da fasahohin nuna wasanni sosai da sosai a kasar Sin, kuma ita da kanta ta iya tsara wakoki da kuma iya fahimtar wakoki sosai da sosai. Lokacin da Wang Feifei ta karbi ziyarar da manema labaru suka yi mata, sai ta gaya musu cewa, ina dalilin da ya sa na rada sunan faifan wakoki da ke daukar muryata da cewa "Mei"? Shi ne saboda ina son yin amfani da furen Mei don bayyana mutane. Furannin Mei ba su tsoron sanyi, sun iya hakuri da wahaloli da kuma iya jurewa sanyi da kankara mai taushi, suna budewa tamkar yadda ake murmushi, amma ba su yi takarar nuna fin kyaun gani a gaban sauran furanni da kuma neman kauna daga wajensu ba, irin wannan halin nagari da suka bayyana ya cancanci da na yi koyi da shi, saboda haka na rada sunan faifan da ke daukar muryata da cewar "Mei"

Wang Feifei ita ma ta himmantar da kanta da halin furen Mei, a ganinta, ta bayyana cewa, ya kamata wata zabiya ta kware sosai wajen fasahar nuna wasanni, sa'anan kuma ta kara tallafinta wajen fasahohin wasanni, har ma ya kamata ta yi kishin wake-wake da fasahohin wasanni sosai da sosai. Bisa kokarin nan ne Wang Feifei ta soma tsara wakoki ita kanta, kuma ta sami sakamako sosai. Ta bayyana cewa, a da, wakokin da na rera, mawallafan wakoki ne suka tsara, yanzu ta hanyar rera wakokin da na tsara ni kaina, na iya rera abubuwan da ke cikin zuciyata.

A lokacin da manema labaru suka kai mata ziyara, ta gaya musu cewa, a mahakar kwal, ana shan wahaloli masu tsanani sosai, kuma ina shan wahaloli da yawa a lokacin da na nuna wasanni domin mahakar kwal, amma a kowane karon da na nuna wasanni dominsu, sai su yi mini maraba sosai, sai na gaya mini cewa, kodayake wahaloli da yawa gare ni, amma dole ne zan ci gaba da rerawa, shi ya sa lokacin da nake nuna wasanni, na ji alheri sosai da sosai. Ta kuma gaya wa manema labaru cewa, lokacin da muka tafi mahakar kwal, ma'aikatan haka kwal ba su taba ganin 'yan wasannin fasaha suka shiga ramukan haka kwal ba, shi ya sa sun burge sosai, sun ja hannuna sosai, kuma sun rera wakoki tare da mu, kodayake iskar da ke bakin ramukan haka kwal na da karfi sosai, amma mu rera musu wakoki cikin himma da kwazo.

Bisa matsayinta na wata zabiya, Wang Feifei tana kaunar al'adun gargajiyar kasar Sin da wake-waken gasgajiyar kasar Sin sosai da sosai. Wani lokaci, ta tafi kasashen waje don nuna wasanni, amma mutanen kasashen waje da yawa ba su san kasar Sin sosai ba a yayin da suke begen fahimtar kasar Sin, sai Wang Feifei ta yi fatan za ta gaji da kuma yadu da al'adun kasar Sin ta hanyar wakokinta, tana son zama wani jakadan kasar Sin wajen wake-wake da al'adu. (Halima)