Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-07 17:00:28    
Halin da Somaliya ke ciki yana kasa yana dabo

cri

Bayan kazamin fada da aka shafe watanni da dama ana yi, kwanan nan kungiyar kotunan musulunci, wato dakarun addini na kasar Somaliya ta lashe 'kawancen maido da zaman lafiya da yaki da ta'addanci' wanda ke kunshe da mayaka na rukunoni iri iri, har ma ta cimma nasarar mamaye birnin Mogadishu, babban birnin kasar. Mogadishu wanda ya yi shekaru har 15 yana rarrabuwa a karkashin mulkin kungiyoyin mayaka daban daban ya sami dinkuwa daga karshe. Game da ko al'amarin yana da kyau ko ba shi da kyau, bangarori daban daban ba su sami daidaituwar baki ba.

A ganin Mr.Ali Mohammed Gedi, firaministan gwamnatin wucin gadi na kasar Somaliya, al'amarin nan yana da kyau. ya bayyana a ran 6 ga wata cewa, mamaye birnin Mogadishu da dakarun addini suka yi wani mataki ne mai matukar kyau da aka yi a kan hanyar neman tabbatar da zaman lafiya a Somaliya, yana kuma sa ran yin shawarwari da dakarun. Ya kuma kara da cewa, ya fi son tuntubar dakarun addini, sabo da 'madugan mayaka ba su son nuna amincewa ga gwamnatin wucin gadi, kuma ba su son ganin zaman lafiya'. Bayan haka kuma, dan majalisa kuma tsohon ministan watsa labaru na kasar, Mohamud Jama ya fi darajanta al'amarin. Ya ce, mamaye birnin Mogadishu da dakarun addini suka yi wani muhimmin ci gaba ne da aka samu don neman kawo karshen yakin basasa da aka shafe shekaru da dama ana yi a Somaliya, wanda kuma zai kawo damar samun zaman lafiya a Somaliya. Idan dakarun za su iya karfafa ikonsu a birnin, to, gwamnatin wucin gadi na Somaliya za ta yi shawarwari tare da bangare daya kawai a maimakon bangarori da dama, wannan kuma zai kawo saukin yin shawarwari, haka kuma zai taimaka wajen kafa wani tsarin siyasa mai inganci a Somaliya bayan da aka rasa samun wata sahihiyar gwamnati a kasar a shekaru 15 da suka wuce.

Amma duk da haka, wasu ba su rike da ra'ayi mai kyau a kan al'amarin. Suna damuwa da kara karfinta za ta yi idan kungiyar kotunan musulunci wadda ake ganin tana da nasaba da kungiyar al-Qaeda ta mamaye birnin Mogadishu, kuma abin zai sa Somaliya ta zama wani dandali na 'yan ta'adda, har ma zai sa kasar Somaliya za ta fada cikin hannun kungiyar al-Qaeda da ke karkashin jagorancin Bin Laden. Wani masanin Amurka a kan batun Somaliya, Omar Jamal ya ce, nasarar da 'yan gwagwarmayar Islama suka samu a birnin Mogadishu za ta zama wani muhimmin al'amari a tarihin kasar Somaliya, kuma 'al'amarin daidai yake da yadda kungiyar Taliban ta sami tasowa a kasar Afghanistan'. Ban da wannan, ko da yake kakakin majalisar gudanarwa ta Amurka bai yi sharhi a kan al'amarin kai tsaye ba, amma a bayane ne ya bayyana cewa, 'ba a son ganin Somaliya ta zama mabuyar 'yan ta'adda na kasashen waje."

Wasu mutane kuma suna damuwa da kara haddasa rikicin dakaru da za a yi bayan da dakarun addini suka mamaye Mogadishu.

Amma duk da haka, dakarun addini suna son kashe damuwar mutane. Sharif Shaikh Ahmed, jagoran kungiyar kotunan musulunci ya bayyana a ran 6 ga wata cewa, ba su son kafa wata kasa mai mulkin musulunci na salon 'Taliban' a Somaliya, a maimakon haka dai, za su mika ikon kasar a hannun jama'ar Somaliya, don su tabbatar da makomar kasar.

Tambaya dai a yanzu ita ce shin mene ne matsayin da jama'a suka dauka a kan kungiyar kotunan musulunci? Manazarta suna ganin cewa, idan an tabbatar kungiyar tana taka rawa mai yakini a wajen aikin shimfida zaman lafiya a Somaliya, to, mai yiwuwa ne kungiyar za ta mayar da ikon birnin Mogadishu a hannun gwamnatin wuci gadi, kuma za a iya sa aya ga yakin basasa wanda ke damun somaliya shekaru da dama ke nan. Amma a sa'i daya kuma, idan an tsaya kan daukarta a matsayin wata kungiyar masu tsattsauran ra'ayi ta musulunci, to, watakila dai za ta dauki wani matsayi na adawa na gwamnatin wucin gadi, mai yiwuwa ne kuma, Somaliya za ta kara shiga cikin tashin hankali. (Lubabatu Lei)