 Assalamu alaikum ! Jama'a masu karatun shafinmu na Internet , ga shirinmu na musamman na "Duniya ina labari" na yau mai lakabin haka: Kasar Sin tana kokarin sa kaimi kan yalwatuwar masana'antun software .
Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , kwanan baya a nan birnin Beijing , wani jami'in Ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya bayyana cewa , nan gaba kasar Sin za ta samar da gurbi mai kyau ga yalwatuwar masana'antun software kuma za a kara karfafa hadin gwiwar duniya a wajen nazarta da aiwatar da aikin software .
A gun wani taron da aka yi kwanan baya , Lou Qinjian , mataimakin ministan sadarwa na kasar Sin ya bayyana cewa , a cikin 'yan shekarun da suka shige , yalwatuwar aikin software tana jibintar tsaron kasar Sin a wajen bayanonin sadarwa . Aikin software kuma muhimmin aiki ne dake cikin tattalin arzikin kasar . Saboda haka kasar Sin za ta dauki matakai daban daban don sa kaimi kan yalwatuwar aikin software .
Yanzu masana'antar software ta riga ta zama muhimmin aiki a wajen yin gasar kimiyya da fasahohin zamani . A cikin 'yan shekarun da suka shige , a duk duniya ana kiyaye saurin yalwatuwar software . Kuma ana yin amfani da shi a fannin sha'anin kudi da hanyoyin sadarwa da lissafi da harkokin haraji da sauran fannoni .
Bisa kididigar da aka yi , an ce , a shekarar 2004 yawan kudin da aka samu a wajen sayar da software ya kai dallar Amurka fiye da biliyan 880 , wato ya karu da kashi 11 cikin 100 bisa shekarar 2003.
Masanan fasahohin saftware na kasar Sin sun ce , wannan ne karo na farko da kamfanin software na kasar Sin ya ya sami damar bude kofa ga jarin kasashen waje don su yalwata ayyukan bayanonin sadarwa .

Bisa bayanin da aka yi , an ce , ba da izni ga 'yan kasuwanni na kasashen waje a wajen yalwata aikin software a nan kasar Sin , ba kawai ya iya kara saurin bunkasa ayyukan sadarwa ba , har ma zai kawo tasiri mai kyau ga gyare-gyaren tsarin yalwata software na gwamnatin kasar Sin . Da ya tabo maganar yadda za a warware matsalolin da za a fuskanta a lokacin da ake shigowa da jarin kasashen waje , Mr. Ding ya bayyana cewa , yanzu ya kamata a kyautata manufofin shigo da jarin kasashen waje a wajen yalwata aikin software na kasar Sin . Dole ne gwamnati ta daidaita abubuwan da muke yi bisa halin musamman na 'yan kasuwanni na kasashen waje .
Mr. Wei , mataimakin ministan kasuwanci na kasar Sin ya bayyana cewa , tun da kasar Sin ta shiga cikin Kungiyar Ciniki ta Duniya ta yi alkawarin bude kofar jiragen kasa ga kasashen waje , kuma ta riga ta dauki matakai masu yawa . A farkon wannan shekara , Kwamitin yalwatuwa da gyare-gyare na kasar Sin ya sanar da cewa , za a ba da izni ga 'yan kasuwanni na kasashen waje da su shiga aikin software na kasar Sin ta hanyoyi iri daban daban .
Mr. Su Zhixun , babban manajan Kamfanin fasahohin adadi ya ce , saboda a kasar India da kasar Sin da sauran kasashe matasa akwai fifikon kwadago mai yawa wato albashin da ake biyansu kadan ne , shi ya sa wasu kasashe masu sukuni na Turai da Amurka su kan yi kwangilar wasu ayyukan software ga wadannan kasashe . Nan gaba dole ne mu mai da hankali kan hadin gwiwar kasashen duniya don kara yalwata aikin software.
To, jama'a masu karatun shafinmu , shirin "Duniya ina
labari "da za mu iya kawo muku ke nan a yau . Ado ne ya fasara wannan bayanin . Da haka muke muku sallama tare da fatan alheri .(Ado )
|