Ran 6 ga wata a babban birnin Teheran na kasar Iran, Ali Larijani wakili na farko a gun shawarwarin nukiliya kuma sakatare na kwamitin koli na tsaron kasa ta Iran ya yi shawarwari tare da Javier Solana wakilin kungiyar gammayar kasashen Turai mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro. Bayan shawarwarin, Mr. Larijani ya ce, wannan shawarwarin yana da amfani sosai.
Bisa labarin da muka samu, lokacin da Larijiani ya gana da manema labaru ya ce, don daidaita maganar nukiliya, kasar Iran za ta yi kokari don yin la'akari kan shirin da kasashe biyar na dindindin na kwamitin sulhu da kasar Jamus suka gabatar. Shirin da kasashen shida suka gabatar suna kunshe da abubuwa "masu kyua" da abubuwa "marasa tabbas", kasar Iran za ta yi amsa bayan ta yi nazari sosai a kan su.
|