Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-06 14:36:00    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(01/06-07/06)

cri
An fara aiwatar da shirin raya kasuwar taron wasannin Olympic na nakasassu na shekarar 2008 a ran 5 ga watan Yuni, masana'antu 22 na gida da na waje sun zama abokan yin hadin gwiwa ko kuma masu ba da kudade don taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing. Babban makasudin wannan shiri shi ne yin furofaganda kan kyakkyawar siffa da darajar taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin, da tattara kudi da kayayyaki don taron wasannin Olympic na nakasassu na Beijing da kwamitin wasannin Olympic na nakasassu na kasar Sin da kuma kungiyar wakilan 'yan wasa nakasassu ta kasar Sin da kuma ba da taimako ga masana'antu wajen kara darajar tambarinsu da sunayensu. Akwai wani labari daban da aka ruwaito mana game da taron wasannin Olympic na Beijing, an ce, a ran 2 ga watan Yuni, a cikin wurin shakatawa na Tiantan, hukumar yawon shakatawa ta Beijing ya yi bikin bude babbar gasar daukan hotuna kan Beijing, birnin da zai shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008. A gun wannan babbar gasar, za a bayyana tarihi da al'adu na Beijing da kuma halin da take ciki a yanzu daga dukan fannoni, za a kuma jaddada bayyana surar Beijing a matsayin babban birni na zamani a duniya da kuma ra'ayoyi da matakan da 'yan birnin Beijing suke daukawa don share fage ga taron wasannin Olympic na shekarar 2008.

Ran 30 ga watan Mayu, a Suzhou, an rufe babban taron wasannin motsa jiki na karo na 3 na kasar Sin, wanda aka yi kwanaki 11 ana yinsa. A lokacin babban taron, 'yan wasa sun karya matsayin bajimta na duniya a cikin gasanni 11, yayin da wasu suka karya matsayin bajimta na Asiya a cikin gasanni 5, sa'an nan, wasu sun karya matsayin bajimta na kasar Sin a cikin gasanni 16.

Ran 3 ga watan Yuni, zakarar taron wasannin Olympic na Athens Meseret Defar, 'yar kasar Habasha ta karya matsayin bajimta na duniya na mata na gasar gudun mita 5000 da mintoci 14 da dakika 24 da motsi, ta kuma sami lambar zinare a cikin gasar ba da babbar kyauta ta wasannin guje-guje da tsalle-tsalle ta New York saboda makin da ta samu.(Tasallah)