Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-05 17:44:05    
Kasar Sin ta kaddamar da takardar bayani dangane da batun kiyaye muhalli

cri

Ran 5 ga wata "ranar muhallin duniya" ce. A wannan rana gwamnatin kasar Sin ta bayar da takardar bayani dangane da batun "kiyaye muhallin kasar Sin daga shekarar 1996 zuwa ta 2005, wanda ya bayyana kokarin da kasar Sin ta yi cikin shekaru 10 da suka wuce ta hanyoyi daban-daban domin kiyaye muhalli. Takardar ta ce, yanzu an sami sassauci wajen yunkurin kazancewar muhalli da lalacewar halittu masu rai, amma har ila yau ana fuskantar matsalar muhalli mai tsanani. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayani da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.

Wannan takardar bayanin da ofishin ba da labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayar a wannan rana ta zama takardar bayani ta 2 da kasar Sin ta bayar cikin shekaru 10 da suka wuce kan batun kiyaye muhalli wadda take kunshe da babbaku fiye da dubu 16, wadda kuma ta kasu kashi 12 ciki har da yin rigakafin kazancewar masana'antu, da gama gwiwar kasashen duniya domin kiyaye muhalli. A lokacin da ofishin ba da labaru na majalisar gudnarwa ta kasar ya kaddamar da wannan takardar bayani, kuma ya kira taron manema labaru a wannan rana a nan birnin Beijing, inda ya gayyaci Mr. Zhu Guangyao, mataimakin shugaban babbar hukumar kiyaye muhalli ta kasar Sin da ya bayyana wa manema labaru na gida da na kasashen waje hakikanan abubuwan da ke cikin wannan takardar bayani.

Takardar bayanin ta bayyana cewa, tun daga karshen shekaru na 70 na karni na 20 zuwa yanzu, bisa bunkasuwar tattalin arzikin da kasar Sin ta samu da sauri, matsalolin muhalli da kasashe masu ci gaba suka gamu da su a lokacin da suka mayar da kasashensu su zama kasashe masu masana'antu su ma sun bullo a kasar Sin, sabanin da ke tsakanin muhalli da bunkasuwa sai kara tsanani yake a kowace rana. Mr. Zhu ya ce, kusan shekaru 10 da suka wuce ya zama lokacin da kasar Sin ta kara zuba kudi mafi yawa domin kiyaye muhalli.

"Cikin shekaru 10 da suka wuce, yawan kudin da kasar Sin ta ware musamman domin yin rigakafin kazancewar muhalli yana nan yana ta karuwa a kowace shekara, yawan kudin da aka ware a shekarar da ta wuce a wannan fanni ya kai kudin Sin Yuan biliyan 238.8, wato ya kai kashi 1.31 cikin 100 bisa na GDP wato jimlar kudin da aka samu daga aikin kawo albarkar kasa, wannan adadi da kyar ake samun irinsa a kasashe masu tasowa."

Ban da wannna kuma kasar Sin ta shiga yarjeniyoyin kasashen duniya fiye da 50 dangane da kiyaye muhalli ciki har da "Yarjejeniyar shirin sauye-sauyen yanayin sama ta M.D.D." da "Takardar shawara ta Kyoto", kuma tana yin kokarin aiwatar da hakkokin da aka tsara cikin wadannan yarjeniyoyi.

Sa'an nan kuma takardar bayani ta bayyana cewa, ko da yake gwamnatin kasar Sin da jama'arta sun yi matukar kokari domin kiyaye muhalli, amma sabo da kasar Sin wadda take cikin lokacin kara saurin mai da kasar da ta zama mai masana'antu kuma mai kunshe da alkaryu da garuruwa na zamani, kuma tana cikin lokacin da take kara gamuwa da sabani mai tsanani a tsakanin karuwar tattalin arziki da kiyaye muhalli, shi ya sa har ila yau tana cikin matsanancin hali wajen muhalli. A lokacin da Mr. Zhu ya tabo wannan batu ya bayyana cewa,"Dole ne mu gane sosai cewa, har ila yau halin da ake ciki a kasar Sin yana da tsanani wajen muhalli. A wurare da yawa ba a daidaita tsoffin matsalolin muhalli ba tukuna sai sabbin matsalolin sun bullo." (Umaru)